A lokacin ganawarsa da takwaransa na kasar Senegal Sidiki Kaba, Wang ya yabawa kasar Senegal saboda cigaba da goyon bayan da take baiwa kasar Sin game da batutuwan da suka shafi hakkokin kasar Sin game da muhimman muradunta, kana kasar Sin a shirye take ta nuna goyon bayanta ga kasar Senegal wajen samar da hanyar cigaban kasar da kiyaye moriyarta da hakkokinta.
Senegal tana sahun gaba cikin kasashen yammacin Afrika wajen sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya (BRI), kuma a matsayinta na mai taimakawa jagorancin dandalin hadin kan Sin da Afrika (FOCAC), ta bude wani sabon shafi game dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, inji Wang.
A nasa bangaren, Kaba yace BRI, da sauran muhimman kudurori guda 8 dake shafar Afrika wanda shugaba Xi Jinping ya gabatar ya dace da ajandar kungiyar tarayyar Afrika na raya nahiyar nan da shekarar 2063 da manufar bunkasa Senegal wanda shugaban kasar Macky Sall ya gabatar, wanda zai haifar da babbar moriya da kuma samar da muhimmin sakamako na samun moriyar juna tsakanin Sin da Afrika.