in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun mamaye ofisoshin jaridar Daily Trust
2019-01-07 14:12:54 cri

A jiya Lahadi jaridar Daily Trust da ake bugawa a kasar Najeriya ta ba da labarin cewa, sojojin kasar sun mamaye ofisoshinta dake Maiduguri da kuma Abuja tare da kama wakilanta biyu, sakamakon wani sharhi da ta wallafa game da yakin da sojojin kasar ke yi da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Jaridar ta ce, sojojin sun kuma rufe ofishinta dake garin Maiduguri bayan da suka damke editan shiyyar da kuma mai dauko mata da rahotanni.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta umarci sojojin da su fice daga harabar jaridar ta Daily Trust.

Garba shehu ya ce, za a warware rigimar da ta taso tsakanin sassan biyu game da ba da rahotannin rikicin dake faruwa a yankin arewa maso gabashin kasar ta hanyar tattaunawa.

Rahotanni na cewa, mayakan Boko Haram sun halaka kimanin mutane 30,000 tun lokacin da kungiyar ta fara kaddamar da hare-hare a shekarar 2009 da nufin kafa daular Islama a kasar. Ko da a watan Disamba ma, kungiyar ta kai hari garin Baga dake kan iyaka da Jamhuriyar Nijar, da Chadi da kuma Kamaru, inda ta tilastawa daruruwan mutane neman mafaka a garin Mauduguri, fadar mulkin jihar Borno.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China