in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump yace ana kokarin cimma matsaya game da inda za'a shirya tattaunawa tsakanin Amurka da Koriya ta arewa
2019-01-07 10:40:56 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a jiya Lahadi cewa ana kokarin cimma matsaya game da wajen da za'a shirya taron kolin tattaunawa tsakanin Amurka da Koriya ta arewa (DPRK).

"Muna kokarin cimma matsaya game da inda za'a gudanar da taron kolin tsakaninmu da Kim na Koriya ta arewa," Trump ya fadawa 'yan jaridu gabanin ya tashi zuwa Camp David, inda zai tattauna game da batutuwan da suka shafi tsaron kan iyakoki.

Trump ya kara da cewa, Washington da Pyongyang "sun yi tattaunawa mai kyau", amma ya kara da cewa har yanzu takunkuman da aka kakabawa DPRK suna nan daram.

Gwamnatin shugaba Trump ta sha tura wasu tawagogi zuwa wurare daban daban a yankuna daban daban, da suka hada da Asiya, domin tsara tattaunawar da za'a yi a zagaye na biyu tsakanin Trump da Kim Jong Un, shugaban gwamnatin DPRK, in ji wani rahoton tashar talabijin ta CNN.

Trump ya sanar a farkon wannan makon cewa, yana sa ran shiga zagaye na biyu na ganawa da mista Kim a wata ganawa ta kut-da-kut. Ya kara da cewa ya samu wasika '"mai girma" daga shugaban kasar Koriya ta arewan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya fadawa manema labarai a ranar 3 ga watan Janairu cewa, kasar Sin a ko da yaushe ta yi amanna cewa, samun musayar ra'ayoyin mai kyau da kuma kyakkyawar tattaunawa tsakanin Amurka da Koriya ta arewa zai bada babbar gudunmowa wajen warware takaddamar makamashin nukiliyar zirin Koriya da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China