in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan IS sun yi garkuwa da wasu kauyawa 5 a tsakiyar Iraqi
2019-01-07 10:33:40 cri
Mayakan kungiya mai da'awar kafa daular Islama (IS) ta sanar a jiya Lahadi cewa, ta yi garkuwa da wasu kauyawa su 5 inda ta raba su da gidajensu a kusa da birnin Tikrit, babban birnin lardin Salahudin da ke tsakiyar kasar Iraq, wata majiya daga 'yan sandan kasar ce ta sanar da hakan.

Al'amarin ya faru ne da yammaci a lokacin da wasu mayakan IS su 20 suka shiga kauyen Tal-Gseiba a gabashin birnin Tikrit, mai tazarar kilomita 170 a arewacin Baghdad babban birnin kasar Iraqi, Kanal Mohammed Khalil al-Bazi na ofishin 'yan sandan lardin Salahudin ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Wata rundunar tsaron hadin gwiwa ta sojojin Iraqi, da 'yan sanda da jami'an tsaron farin kaya mai suna Hashd Shaabi ta kaddamar da gangamin farautar mayakan masu tsauttsauran ra'ayi da kuma ceto mutanen kauyen da aka yi garkuwa da su, in ji al-Bazi.

Yanayin tsaro a Iraqin yayi matukar kyautata tun bayan da dakarun tsaron Iraqi suka samu galaba kan mayakan IS masu tsattsauran ra'ayi a duk fadin kasar a shekarar 2017.

Sai dai kuma, kananan kungiyoyi da daidaikun mayakan masu tsattsauran ra'ayin suna sake hallara a wasu biranen yankunan kasar, kana suna kokarin kaddamar da hare hare kan jami'an tsaro da fararen hula duk da irin yunkurin da jami'an tsaron ke yi a lokuta daban daban don murkushe 'yan ta'addan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China