in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi nasarar kama mutane 5,000 a yakin da ta ke da cin hanci
2019-01-07 10:12:23 cri
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Sin ta ce, daga shekarar 2014 zuwa ranar 30 ga watan Nuwamban shekarar 2018 da ta gabata, ta yi nasarar tusa keyar kamanin mutane 4,997 daga sama da kasashe da yankun 120 zuwa gida domin su fuskanci hukunci.

Hukumar ta ce, daga wadanda aka kama 1,015 sun taba kasancewa 'yan JKS ne ko kuma ma'aikatan hukumomin gwamnati.

A cikin wannan lokaci da ake batu, hukumar ta yi nasarar kwato kudaden da suka kai Yuan biliyan 10.51, kwatankwacin dala miliyan 1,530 da mutane suka tara ta haramtacciyar hanya.

Bayanai na cewa, daga cikin kusan mutane 5,000 da aka kama, 56 daga cikinsu na daga cikin mutane 100 da mahukunatan kasar Sin ke nema ruwa jallo, bisa hannun da suke da shi a manyan laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China