Rundunar sojojin kasar ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi cewa, an kashe janar Obi ne, wadda kungiyarsa ke damun al'ummomin Manfe da Okoyong da Bahuo Ntaida Bachou Akagbe da kua Nchemba ne a safiyar ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2019.
A cewar sanarwar, samamen da sojojin bataliyar dake kai daukin gaggawa(BIR) suka kaddamar shi ma ya kai ga halaka janar Eyong, daya daga cikin kwamandojin mayakan 'yan awaren. An kuma lalata sansanoninsu tare da gano ko lalata wasu makamai
Samamen da sojojin suka kaddamar na zuwa ne kimanin mako guda bayan da shugaba Paul Biya na kasar ta Kamaru, ya gargadi mayakan yayin jawabin karshen shekara da ya saba gabatarwa al'ummar kasar, cewa zai sanya kafar wando guda da mayakan muddin suka ki ajiye makamansu don bin hanyar da ta dace.(Ibrahim)