"Ba zai yiwu a sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi ba. Muna dukkan shirye shiryen da suka dace amma har zuwa yanzu ba mu kammala komai da komai ba," in ji Corneille Nangaa, ya sanar da hakan ne a jiya Asabar ba tare da bayyana takamammiyar ranar da za'a sanar da sakamakon zaben ba.
"A makon gobe muke sa ran fitar da sakamakon," in ji shi.
A cewar Nangaa, hukumar zaben ta CENI ta karbi kashi 45 zuwa 48 bisa 100 ne kadai na takardun kada kuri'ar a duk fadin kasar.
A ranar 30 ga watan Disamba ne aka gudanar da babban zaben a fadin kasar, in bada wasu birane 3 wadanda aka dage zaben sakamakon matsalar rashin tsaro gami da barazanar barkewar annobar cutar Ebola, wadda ta yi mummunar barna a yankuna masu yawa na arewacin lardin Kivu dake gabashin kasar ta Kongo. (Ahmad Fagam)