Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Aeya Kwamando Ibikunle Daramola, ne ya bayyana hakan a Abuja, ya ce an kai harin ne a ranar Laraba. A cewar rundunar, sashen na ta ya aike da Jiragen Helikwafta guda biyu, inda suka kai hari ga 'yan ta'addan har suka lalata makoyar na su.
Hari na biyu da aka kaiwa 'yan ta'addan ya tilasta ma 'yan ta'addan fitowa daga maboyar na su, inda a nan ma aka kashe da dama daga cikin su. Daramola ya ce, majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa, jagoran 'yan ta'addan yana daga cikin wadanda aka kashe a cikin harin.
Ya ce, rundunar na su za ta ci gaba da yin aiki tare da dakarun kasa da sauran sassan hukumomin tsaro, domin kai hare-haren, domin tabbatar da dawo da zama lafiya a duk Jihohin da ake fama da rashin zaman lafiyan na arewa maso yamma. (labarin da aka samu daga jaridar Leadership)