in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantakar Sin da AU tana mataki mafi daraja a tarihi, in ji ministan wajen Sin
2019-01-05 16:13:32 cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar tarayyar Afrika (AU) a halin yanzu ta kai matsayin dangantaka mafi daraja a tarihi.

Wang Yi, ya bayyana hakan ne a lokacin wata ganawa da ya yi da shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU Moussa Faki Mahamat, a helkwatar kungiyar ta AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Ya bayyana AU a matsayin wata sabuwar hanyar hadakan kasashen Afrika, da dogaro da kai, da kuma samun bunkasuwa, Wang ya ce, bangarorin biyu za su yi aiki tare wajen tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron kolin Beijing na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC, da mayar da hankali kan muhimman fannoni 4 na hadin gwiwar Sin da Afrika, da suka hada da batun zaman lafiya da tsaro, da kiwon lafiya, da kuma taka rawa a harkokin kasa da kasa.

Kasar Sin a shirye take ta yi musayar irin nasarorin ci gaban da ta samu wajen raya manyan muradun ci gaba na kasashen Afrika, musamman wajen yin hadin gwiwa don aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da ajandar AU ta raya Afrika nan da shekarar 2063, in ji Wang.

A nasa bangaren, Faki ya ce dangantakar dake tsakanin Afrika da Sin hadaddiya ce, abokantaka ce, kakkarfar dangantaka ce, kuma dangantakar moriyar juna ce.

Faki ya ce, AU tana maraba da irin taimakon da kasar Sin ke bayarwa wajen bunkasa samar da muhimman kayayyakin more rayuwa, da aikin wanzar da zaman lafiya a fadin nahiyar ta Afrika.

Ya kuma nanata aniyar kungiyar ta AU wajen ci gaba da kyautata mu'amala da tuntubar juna tsakaninta da bangaren Sin, da kuma aiwatar da muhimman ayyuka 8 da shugaba Xi Jinping ya gabatar wadanda za su kara ingiza hadin kan dake tsakanin Sin da Afrika.

Faki ya ce, AU a shirye take ta kara karfafa hadin gwiwarta da kasar Sin, tare da yin hadin gwiwa wajen kiyaye ka'idojojin gamayyar kasa da kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China