in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burkina Faso ya yi alkawarin karfafa hadin gwiwa da Sin
2019-01-05 15:43:18 cri

Shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, a jiya Juma'a, ya yi alkawarin kara karfafa dangantaka tsakanin kasarsa da kasar Sin.

Kabore, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, wanda ke ziyarar aiki a kasar.

Shugaban ya nanata cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, ya ce kasarsa a shirye take ta karfafa dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin karkashin manufar nan ta kasar Sin daya tak.

Kabore ya yabawa irin taimakon da kasar Sin ke baiwa kasarsa a fannonin ci gaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma, yana mai cewa, mutanen Burkina Faso suna kara kyakkyawar fatar karfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba.

A nasa bangare, jami'in kasar ta Sin ya ce, matakin da shugaba Kabore ya dauka na farfado da dangantakar diplomasiyya dake tsakanin kasarsa da kasar Sin ya samu gagarumin goyon bayan al'ummar kasar Burkina Faso, kana matakin ya samu karbuwa daga nahiyar Afrika baki daya.

Tarihi zai shaida cewa, farfadowar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ya dace da babbar moriyar kasar Burkina Faso da mutanen kasar, in ji mista Wang.

Ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Burkina Faso wajen zurfafa hadin gwiwa don wanzar da zaman lafiya da tsaro.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China