Yau hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta bayyana cewa, tun bayan da na'urar bincike ta Chang'e-4 da na'urar binciken duniyar wata samfurin Yutu-2 ko Jade Rabbit-2 suka rabu da misalin karfe 5 na yammacin yau, na'urar ta fara aikin bincike kamar yadda aka tsara, kuma ta aiko da hotunan da ta dauka zuwa doron duniyarmu daya bayan daya.
Daga baya tauraron Chang'e-4 zai gamu da matsalar zafi mai tsanani, har na'urar Yutu-2 za ta daina aiki, sai zuwa ranar 10 ga wata kafin za ta fara aiki.(Jamila)