in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fannoni guda 5 da Xi Jinping ya gabatar a jawabinsa sun kasance sabon tsarin dokoki na neman dunkulewar kasar Sin ta hanyar lumana
2019-01-04 14:37:50 cri

A farkon sabuwar shekarar da muke ciki a nan birnin Beijing, an shirya wani gagarumin taro, don tunawa da cika shekaru 40 da aikewa da "wasika ga 'yan uwa mazauna Taiwan". Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi kan alakar dake tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan, inda ya jaddada cewa, tabbatar da dunkulewar kasar Sin baki daya, nauyi ne dake kan wuyan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da gwamnati da jama'ar kasar, kuma ya zama wajibi kasar Sin ta dinke waje guda, kuma ko shakka babu za a cimma wannan burin a yunkurin farfadowar al'ummar kasar.

Manazarta sun nuna cewa, a yayin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya yi kira ga Sinawa dake gabobin biyu, da wadanda ke kasashen ketare, da su yi kokarin inganta ci gaban alakar dake tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan, da yunkurin dunkulewar kasar Sin waje guda ta fannoni guda biyar, wato su hada karfi don neman farfadowar al'umma, da neman shirin Taiwan bisa manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu", da tsayawa kan manufar Sin daya kacal, da zurfafa ci gaban gabobin biyu tare, da kuma tabbatar da hadin kan 'yan uwa na gabobin biyu da dai sauransu.

Wadannan fannoni guda biyar sun nuna hanya mai dacewa da za a bi, wajen ciyar da alakar dake tsakanin gabobin biyu gaba. Ba kawai sun sanar da burin kasar Sin na neman dunkulewar kasar waje guda, da farfado da al'ummar kasar ba, har ma sun nuna cewa, babban yankin kasar Sin na fatan yin shawarwari na zaman daidaiwa daida tare da bangarori daban daban na Taiwan, kan tsara shirin Taiwan bisa manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu". Kana yana fatan zurfafa aikin neman ci gaba tare a tsakanin gabobin biyu ta fuskokin tattalin arziki, da al'adu da aikin jinya da kuma ba da tabbaci kan zamantakewar al'umma. A sa'i daya kuma, sun yi gargadi mai tsanani cewa, ba za a samar da dama ga duk wasu ayyukan kawo baraka da nufin neman 'yancin Taiwan ba.

"Matsalar Taiwan ta samu ne sakamakon rashin ci gaban al'umma, dole ne a kawo karshen matsalar bisa farfado da al'umma." Maganar da shugaba Xi Jinping ya ambata, ta samu amincewar Sinawa baki daya.

Bayan yakin Tabar Opium na shekarun 1840, kasar Sin ta shiga hali mai tsanani, har ta kai ga fuskantar manyan matsaloli a cikin gida da ma ketare, hakan ya sa kasar Japan ta mamaye Taiwan na tsaron rabin karni. Daga baya kuma, an yi dauki ba dadi tsakanin gabobin biyu, sakamakon yakin basasa da tsoma baki da sauran kasashen suka yi.

Amma yanzu babban yankin kasar Sin ya kasance na biyu a fannin tattalin arziki a duniya a cikin 'yan shekaru a jere, kuma gudumowar da take bayarwa kan karuwar tattalin arzikin duniya ya wuce kashi 30 cikin dari. Kasar Sin ta sake komawa matsayi na babbar kasar gargajiya a tarihi, kuma ko shakka babu an shigar da batun Taiwan cikin manyan ajandarta.

A cikin wadannan fannonin guda biyar da shugaba Xi Jinping ya gabatar, an tabbatar da cewa, kamata ya yi bangarori daban daban na gabobin biyu su yi kokarin neman shirin Taiwan na "Kasa daya, tsarin mulki iri biyu", wanda ya kasance tsarin mafi dacewa na kasar Sin wajen gudanar da harkokin cikin gida a idannun kasashen duniya. Shirin Taiwan na "Kasa daya, tsarin mulki iri biyu" zai banbanta da na Hong Kong da Macau, zai kuma kula da moriyar al'ummar gabobin biyu sosai, bisa tushen tabbatar da mulkin kai, tsaro da kuma moriyar ci gaba na kasar. Za a girmama da ba da tabbaci sosai ga Taiwan kan matsayi, da tsarin al'umma, da hanyar zaman rayuwa, da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China