in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar ministan wajen Sin zuwa Afirka za ta karfafa alakar Sin da Afirka
2019-01-03 20:57:07 cri

Yanzu haka ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi yana nahiyar Afirka, inda ya fara wata ziyarar aiki daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2019. Wannan ziyara dai wata dadaddiyar al'ada ce ta tsawon shekaru 29 da ko wane ministan harkokin wajen kasar Sin ke fara ziyartar kasashen Afirka a farkon ko wace sabuwar shekara.

Wannan mataki ya kara nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora kan alakarta da nahiyar Afirka, da ma kasashe masu tasowa. Haka kuma matakin ya kara jaddada kudurin kasar Sin na samun ci gaba tare gami da kyakkyawar makoma.

A yayin rangadin da zai kai shi kasashen nahiyar hudu, Wang kana mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, zai tattauna da shugabannin Afirka kan yadda za a aiwatar da matakan da aka tsara a taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da ya gudana cikin watan Satumban shekarar 2018 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Kasar Sin ta kara tabbatar da cewa, ita sahihiyar kawa ce kuma abokiyar hadin gwiwar nahiyar Afirka, bisa ga sahihan manufofi da irin sakamako na zahiri da imanin da take nunawa.

Bugu da kari, kasar Sin tana mutunta zabin al'ummar Afirka na bin hanyar ci gaban da ta dace da yanayinsu, haka kuma ba ta taba tilasta musu yin wani abu ko gindaya musu wani sharadi ba. Kana idan suka fuskanci wani kalubale ko matsaloli, kasar Sin ta kan nemi hanyar ba su taimako ta hanyar da ta dace ta hanyar tattaunawa da abokan huldar ta Afirka.

A shirye kasar Sin ta ke ta taimakawa Afirka, a lokacin da bukatar hakan ta taso. Cikin gomman shekaru ke nan a jere, kasar Sin tana tura tawagar ma'aikatan lafiya zuwa kasashen Afirka domin yakar cututtuka, baya ga masana aikin gona da samar da taimakon kudi da kwarewa da take bayarwa domin farfado da ababan more rayuwa da kawar da talauci.

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin ce ta farko da ta taimaka a lokacin da aka samu barkewar annobar cutar Ebola a yammacin Afirka da lokacin da mummunan yunwa ta shafi gabashin Afirka.

Yayin taron FOCAC na shekarar 2015 da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afitka ta kudu, kasar Sin ta yi alkawarin samar da dala biliyan 60, kana shirye-shiryen hadin gwiwa guda 10 da ta samar sun taimakawa mazauna kasashen nahiyar.

Tagwayen titunan mota da layukan dogo da tashoshin jiragen sama da na ruwa da filayen masana'antu da kasar Sin ta gina a sassa daban-daban na nahiyar, sun taimaka wajen hade nahiyar tare da kara karfinta na masana'antu.

A bangaren musayar al'ummomi, tawagar likitocin kasar Sin, da cibiyoyin al'adu da na Confucius sun kasance manyan kafofin sadarwa wajen karfafa fahimtar juna. An kuma bullo da wani shiri na nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kasar Sin a kasashen Afirka, inda ake nishadantar da mazauna yankunan.

Ziyarar da ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya fara a jajiberin sabuwar shekara, za ta taimaka wajen ganin an aiwatar da shirye-shiryen hadin gwiwa da aka tsara yayin taron FOCAC na shekarar 2018 da ya gudana a birnin Beijing, wanda ya shafi fannonin masana'antu, ababan more rayuwa, saukaka harkokin cinikyayya, kare muhalli, horo da kiwon lafiya.

Ana fatan shiryen-shiryen za su bude wani sabon babi kan alakar dake tsakanin Sin da Afirka a cikin shekaru uku masu zuwa da ma gaba, a wani mataki na gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China