in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin tana son hada kai tare da Masar domin ciyar da Afirka gaba
2019-01-03 20:12:58 cri

Yau Alhamis kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a gun taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, har kullum kasar Sin tana mai da hankali matuka kan alakar dake tsakaninta da kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU, haka kuma tana son hada kai tare da kasar Masar wadda ke rike da shugabancin karba karba na AU domin ciyar da nahiyar Afirka gaba cikin lumana.

Jami'in ya yi nuni da cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, har kullum ministan harkokin wajen kasar Sin ya mayar da kasar Afirka a matsayin wuri na farko da zai fara ziyara a farkon kowace shekara, a makon da muke ciki, mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi yana ziyarar aiki a kasashen Afirka,, haka kuma zai ziyarci hedkwatar kungiyar AU, tare kuma da ganawa da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat. Kasar Sin tana sa ran ziyararsa za ta taka rawa wajen kara karfafa alakar dake tsakanin Sin da Afirka, tare kuma da ingiza zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban kasashen nahiyar ta Afirka, har ta taimaka ga ci gaban kasashe masu tasowa baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China