in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chang'e-4 ya sauka a bayan duniyar wata
2019-01-03 17:27:15 cri

Da misalin karfe 10 da minti 26 na yau, na'urar bincike ta Chang'e-4 da kasar Sin ta kera ta sauka a bayan duniyar wata, sa'an nan, ta aiko wani hoton bayan duniyar wata zuwa gida ta tauraron dan adam na "Queqiao". Kana, wannan shi ne hoton bayan duniyar wata na farko da wata na'urar da bil Adama ya kera ta dauka.

Lamarin da ya nuna cewa, na'urar da kasar Sin ta kera ta sake sauka a duniyar wata, bayan chang'e-3 ta sauka a duniyar wata a shekarar 2013. Kuma kasar Sin ta kasance kasa ta farko wadda ta cimma nasarar saukar da na'urar bincikenta a gaba da kuma bayan duniyar wata. Lalle abin ya kasance babban ci gaba da bil Adama ya cimma a fannin kimiyyar sararin samaniya.

An harba na'urar Chang'e-4 a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2018, daga cibiyar harba taurarin dan Adam dake Xichang na kasar Sin, inda na'urar ta kama hanyar zuwa duniyar wata. Da ma an kera na'urar Chang'e-4 a matsayin wata na'urar Chang'e-3, wadda aka saukar da ita duniyar wata shekaru 6 da suka wuce. Daga bisani, masana kimiyya da fasaha na kasar Sin sun sha tattaunawa kafin su yanke shawarar harba wannan na'urar, wadda da ma ba a da niyyar harbo ta.

Ye Peijian, masanin kimiyyar sararin samaniya na kasar Sin kuma babban jagoran aikin kera tauraron dan Adam na Chang'e-1 yana ganin cewa, an saukar da tauraron dan Adam na Chang'e-4 a barin wata mafi nisa cikin nasara, lamarin ya nuna cewa, an riga an samu cikakkiyar nasarar kammala aikin harba na'urar binciken doron duniyar wata samfurin Chang-4, shi ma ya bayyana cewa, makasudin raya aikin binciken sararin samaniya na kasar Sin shi ne domin kara fahimtar ilmomin dake shafar duniyar sararin samaniya, tare kuma da samun mafita ga ci gaban bil adam a nan gaba, amma ba domin shaidawa al'ummonin kasashen duniya cewa, kasar Sin ta kai matsayin sahun gaba a fannoni daban daban a fadin duniya ba.

Tsarin na'urar bincike ta Chang'e-4 ya yi kusan daidai da na Chang'e-3, amma sakamakon gangarar yanayin kasa dake bayan duniyar wata, da rashin hotunansa na zahiri, akwai matukar wuya da rashin tabbas ga aikin saukar na'urar bincike ta Chang'e-4. Don haka, 'yan kimiyyar kasar Sin sun yi kwaskwarima ga na'urar bisa yanayin kasa da duniyar wata ke ciki, lamarin da ya sa na'urar ta zama na'urar bincike ta farko a duk fadin duniya da ke iya sauka a bayan duniyar wata. Daga baya kuma, na'urar bincike ta Chang'e-4 za ta kara gudanar da bincike kan labarin kasa da albarkatu na duniyar wata daga dukkanin fannoni, don kara samarwa dan Adam bayanai game da duniyar wata.

Da na'urar bincike ta Chang'e-4 ta yi nasarar sauka a bayan duniyar wata, aikin binciken duniyar wata na kasar Sin ya sake jawo hankalin jama'a. Tun bayan da kasar Sin ta harba na'urar bincike ta Chang'e-1 zuwa duniyar wata, kawo yanzu, Sin ta riga ta harba irin wannan na'urori guda hudu. Na'urorin bincike guda uku da aka harba kafin haka, sun sanya aka tabbatar da matakai biyu a gaba kan matakai guda uku na ayyukan binciken duniyar wata na kasar Sin, wato kewayen wata da kuma sauka a wata.

Jigon manufar sararin samaniyar dan Adam, kuma masani a fannin kimiyya na kasar Rasha Tsiolkovski ya taba cewa, "kasa gadon jariri ne na dan Adan, amma duk da haka dan Adan ba su iya zama a cikin wannan gadon jaririn ne har abada." Jimlar nan na da ma'ana kwarai.

Sauyin yanayin da fitar da dumamar iska da sauran ayyukan dan Adam suka haddasa ya sa kaimi ga dan Adam su mai da hankali ga sararin samaniya, da fatan za a fita daga duniyar kasa a nan gaba, da yin rayuwa a sararin samaniya.

Don hakan, duniyar wata mataki na farko ne ga dan Adam wajen neman yin rayuwa a sararin samaniya. Na'urar binciken duniyar wata samfurin Chang'e-4 sabon mataki ne da dan Adam ya yi kokari wajen cimma wannan buri, kana ya shaida cewa, kasar Sin ta yi kokari wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. (Jamila Zhou, Bello Wang, Maryam Yang, Kande Gao, Murtala Zhang, Bilkisu Xin, Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China