in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na'urar bincike ta Chang'e-4 ta sauka a bayan duniyar wata
2019-01-03 14:47:22 cri

Misalin karfe 10 da minti 26 na yau, na'urar bincike ta Chang'e-4 ta sauka a bayan duniyar wata, karo na farko da wata na'urar da bil Adama ya kera ta sauka a bayan duniyar wata.

Bayan tafiyar kilomita dubu 380 cikin kwanaki 26, a yau, 3 ga wata, Chang'e-4 ya kama hanyar sauka a nisa kilomita 15 daga duniyar wata.

Da misalin karfe 11 da minti 40, na'urar Chang'e-4 ta dauki wani hoton bayan duniyar wata, sa'an nan ta aiko shi zuwa gida. Kana, wannan shi ne hoton bayan duniyar wata na farko da wata na'urar da bil Adama ya kera ta dauka.

Sa'an nan kuma, na'urar Chang'e-4 za ta fara ayyukan daidaita kayan aiki da dai sauransu, da kuma raba na'urar sauka da na'urar sintiri a lokacin da ya dace. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China