in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta tsaya kan matsayinta na sanya ayyukan bunkasa aikin gona a sahun gaba
2019-01-03 11:56:12 cri

A yayin taron da kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya a watan Disamban shekarar 2018 kan ayyukan gona da raya yankunan karkara, an maida hankali sosai kan wasu ayyukan da suke shafar aikin gona da raya yankunan karkara da kuma na manoma da dole ne za a kammala su a bana da badi. Galibin jami'an gwamnatin kasar Sin da masana wadanda suke nazarin harkokin aikin gona suna ganin cewa, a yayin taron, an jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa matsayinta na mayar da ayyukan bunkasa aikin gona da raya yankunan karkara a sahun gaba, sannan an gabatar da sabon nauyin karfafa yin gyare-gyare a yankunan karkara bisa sauye-sauyen da ake samu a cikin gida da kuma ketare, sakamakon haka, tabbas ne za a iya tabbatar da ganin kasar Sin ta samu sabon ci gaba wajen zamanintar da yankunan karkara da aikin gona.

Bisa shirin da aka tsara, a lokacin da ake shiga shekarar 2021, wato shekara ce ta cika shekaru 100 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, dole ne kasar Sin ta zama wata al'umma mai matsakaicin karfi. Saboda haka, shekarar 2019 tana da muhimmanci matuka ga wanann shirin da al'ummar kasar Sin take kokarin cimmawa. A yayin taron aikin gona da raya yankunan karkara da aka shirya kwanan baya, wanda manyan direktocin aikin gona na larduna suka halarta, ministan kula da aikin gona da yankunan karkara na kasar Sin Han Changfu ya gabatar da muhimman ayyukan kawar da talauci a yankunan karkara da za a yi a shekarar 2019. Yana mai cewa, "Dole ne a sa ido kan yadda ake aiwatar da shirin yin gwagwarmayar kawar da kangin talauci na tsawon shekaru 3, sannan a yi kokarin tsara sabbin manufofi da daukar sabbin matakai da shirye-shirye, har ma a sa ido kan yadda ake aiwatar da su a kullum domin tabbatar da ganin an cimma burin. Bugu da kari, a maida hankali wajen kawar da kangin talauci ta hanyar bunkasa sana'o'i, da kuma kara sa ido kan wasu yankuna, inda ake da kalubaloli mafi yawa wajen kawar da talauci."

Bisa shirin da aka fitar a yayin taron, wasu ayyukan da dole ne a kammala su a bana da badi su ne, samarwa manoma wani tsabtaccen yananyi nan da shekaru 3 masu zuwa, wato dole ne a sarrafa shara da gurbataccen ruwa, da inganta dakunan bayan gida da inganta muhallin kauyuka. Dole ne a tabbatar da samar da isasshen amfanin gona mai inganci. A waje daya kuma, a kara yin gyare-gyare kan ikon mallakar gonaki, da tsara sabbin shirye-shiryen samar da karin kayayyakin more rayuwa a yankunan karkara da dai makamatansu.

A nan gaba bada dadewa ba, kasar Sin za ta cimma wani burinta, wato mutane wadanda suke fama da talauci ba za su nuna damuwa ba wajen samun isashen abinci da tufafi da ilmin tilas da jinya da kuma wurin kwana mai inganci. Game da wannan burin, shehun malami Chen Qianheng na jami'ar koyon ilmin aikin gona ta kasar Sin yana ganin cewa, ba da aikin jinya shi ne wani muhimmin burin da za a yi kokarin cimmawa.

"Kawo yanzu, an kusan kawar da matsalolin rashin abinci da tufafi ga wadanda suke fama da kangin talauci, amma wasu sun koma halin fama da talauci sakamakon rashin lafiya mai tsanani, wannan matsala ce mai tsanani dake kasancewa a gabanmu. Yaya za a iya mayar da wasu kudaden da mutane wadanda suka kamu da wata cuta mai tsanani sosai suka kashe, sannan ko gwamanti za ta iya sayen wasu inshorar lafiya irin ta kasuwanci ga wadanda suke fama da talauci ko a'a, su ne matsalolin da ya kamata a daidaita su."

Wani muhimmin batu daban da aka tattauna a yayin taron da kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya a watan Disamban shekarar 2018 kan ayyukan gona da raya yankunan karkara, shi ne kara yin gyare-gyare a yankunan karkara. A yayin taron, an nuna cewa, za a kara yin gyare-gyare a yankunan karkara, ciki har da yin gyare-gyare kan ikon mallakar gonaki, sannan za a sabunta salon bunkasa aikin gona, da inganta ka'idojin kare da kuma tallafawa aikin gona. Mr. Han Changfu, ministan kula da aikin gona da yankunan karkara na kasar Sin ya jaddada cewa, za a kara yin gyare-gyare kan ikon mallakar filin gina gidan kwana na manoma kamar yadda ya kamata.

"Bisa hakikanin halin da ake ciki yanzu, za a hanzarta aikin yin gyare-gyare kan ikon mallakar filin gina gidan kwana na manoma, kuma za a fitar da wasu sabbin manufofi da matakai domin tabbatar da ganin an kusan kammala aikin yin rajistar ikon yin amfani da filin gina gidan kwana a yankunan karkara a shekarar 2020. "

A bana da badi, kasar Sin za ta shiga wani muhimmin lokaci, wato a lokacin da take kokarin cimma buri na tabbatar da ganin ta zama wata al'umma mai matsakaicin karfin tattalin arziki, tana fuskantar wasu kalubaloli masu tsanani wajen cin nasarar kawar da kangin talauci da bunkasa yankunan karkara. Ana da imani cewa, bisa sabon shirin da kwamitin kolin JKS ya fitar da kokarin kowa da kowa, za a iya sauke nauyin dake bisa wuyansa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China