in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Al-Qaida sun tsananta kai hare hare kan 'yan tawayen dake biyya ga Turkiyya a arewacin Syria
2019-01-03 10:50:55 cri
Mayakan dake da alaka da kungiyar al-Qaida sun kama wasu garuruwa 13 a yakin da suke da 'yan tawayen dake samun goyon baya daga Turkiyya dake arewacin kasar Syria, bayan da 'yan tawayen suka ayyana shirinsu na yakar mayakan dake da alaka da kungiyar ta al-Qaida, da kuma yunkurin da suke na kwace ikon dukkan yankunan daga hannu mayakan, gidan talabijin na pan-Arab al-Mayadeen TV ne ya bada rahoton a jiya Laraba.

Hayat Tahrir al-Sham (HTS), wani reshe ne na kungiyar Nusra Front dake da alaka da al-Qaida, ta kaddamar da hare hare masu yawa a kauyuka a ranar Laraba, kana ta yi nasarar cigaba da kaddamar da yakin da take yi kan mayakan dake goyon bayan 'yan tawayen National Liberation Front (NLF), dake biyayya ga mayakan da Turkiyya ke tallafawa, a yammacin lardin Aleppo dake gabashin kasar Syria, kamar yadda rahoton ya bayyana.

A nata bangaren, a sanarwar kungiyar ta NLF, ta bukaci 'yayan ta da su kara daura damara da zama cikin shirin ko ta kwana domin tunkarar mayakan HTS da kuma kwace ikon dukkan yankunan dake karkashin mayakan dake da alaka da kungiyar al-Qaida a yammacin birnin Aleppo.

Haka zalila, hukumar kare hakkin dan adam dake Syria ta ce, gwamman mutane da mayakan ne aka hallaka a cikin sa'oi 24 da fara gwabza yakin, wanda aka fara shi a wanna makon. Kungiyar ta kara da cewa, ana fadada yakin da take yi zuwa yankunan dake kusa da lardin Idlib a arewa maso yammacin kasar Syria. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China