Wa'adin aikin kasashen biyar ya fara ne daga ranar 1 ga watan Janairun bana har zuwa ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2020. Sauran wasu kasashe biyar da ba na dindindin ba a kwamitin sulhun sun hada da Poland, da Kwadibwa, da Kuwait, da Peru gami da Equatorial Guinea, wadanda wa'adin aikinsu zai cika a karshen shekarar da muke ciki.
A halin yanzu, kwamitin sulhun MDD na kunshe da membobi 15, ciki har da zaunannun membobi guda biyar, da suka hada da Sin da Faransa da Rasha da Birtaniya gami da Amurka, yayin da sauran wasu kasashe goma wadanda ke zama membobin da ba na dindind ba. Tsawon wa'adin aikin kasashe membobin da ba na dindindin ba shine shekaru biyu, kuma kowace shekara za'a canja guda biyar, amma ba zasu yi tazarce ba. Za'a zabi kasashe membobin da ba na dindindin ba bisa nahiyoyin da suke, wato guda uku daga Afirka, guda biyu-biyu daga yankin Asiya da Pasifik, da na Latin Amurka da yankin Caribbean, da yankin yammacin Turai da sauran wasu yankuna, sa'annan guda daya daga yankin gabashin Turai.(Murtala Zhang)