in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taiwan ba zai rasa damar shiga aikin farfadowar al'ummar kasar Sin ba
2019-01-02 19:48:19 cri

Yau ranar 2 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabin a gun taron tunawa da cika shekaru 40 da aka aike "wasika ga 'yan uwa mazauna Taiwan", inda ya waiwayi ci gaban alakar dake tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan a cikin shekaru 70 da suka gabata wato tun bayan da sassan biyu suka rabu da juna a shekarar 1949, haka kuma ya gabatar da manufa a fannoni biyar domin ingiza ci gaban alakar sassan biyu cikin kwaciyar hankali a sabon zamanin da ake ciki da kokarin inganta manufar kasar Sin daya tak cikin lumana, kana ya jaddada cewa, ya zama wajibi a tabbatar da kasancewar kasar Sin daya, kuma ko shakka babu za a cimma wannan burin, a don haka tabbas lardin Taiwan na kasar Sin zai shiga aikin farfadowar al'ummar kasar, a sa'i daya kuma lamarin zai kawo wa kasashen duniya karin damammakin samun ci gaba.

Jawabin shugaba Xi ya nuna babban burin kasar Sin na tabbatar da wanzuwar kasar Sin daya tak cikin lumana, haka kuma ya yi kashedi ga masu yunkurin kawo barakar Taiwan da wasu kasashen ketare wadanda ke da kulla wannan makarkashiya ta hanyar tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin, wato jawabin da shugaba Xi ya gabatar ya bayyana cewa, jam'iyya mai mulkin kasar Sin wato jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suna nacewa ga aniyarsu ta kiyaye 'yanci da cikakken yankunan kasar, wannan shi ne manufa mafi muhimmanci da kasar Sin za ta aiwatar yayin da take kokarin tabbatar da burin wanzuwar kasar daya tak a sabon zamanin da ake ciki.

A shekaru 40 da suka gabata, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya aike da "wasika ga 'yan uwa mazauna Taiwan", a wancan lokaci, jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta riga ta sake samun dukkan iko a MDD, kusan daukacin kasashen duniya sun amince da cewa, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin wanda ba zai yiyu ba a raba shi daga yankin kasar Sin. A wancan lokaci, wasikar ta jaddada cewa, kasar Sin daya kacal ce a duniya, kuma ta gabatar da wasu matakai, misali kawo karshen kiyayyar soja, da fara sadarwa da kasuwanci da jirga-jirga, da kuma kara habaka cudanyar dake tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan, domin ciyar da alakar, tare kuma da cimma burin wanzuwar kasar Sin data tak cikin lumana.

A cikin jawabin, shugaba Xi ya waiwayi sakamakon da aka samu wajen sadarwa da kasuwanci da kuma jirga-jirga a cikin shekaru 70 da suka gabata, haka kuma ya waiwayi shawarwarin da sassan biyu suka yi bisa tushen matsaya guda da suka cimma a shekarar 1992, da manufofin da ya kamata a aiwatar da su yayin da ake kokarin daidaita batun Taiwan cikin lumana da fahimta da goyon baya na zamantakewar al'ummar kasashen duniya kan batun, da kuma ci gaban da aka samu wajen yaki da makarkashiyar kawo baraka ga yankin kasar Sin, a karshe dai ya bullo da cewa, ba zai yiyu ba a canja hakikanin yanayin da ake ciki wato Taiwan wani bangare ne na yankin kasar Sin, gabobi biyu na zirin Taiwan suna cikin kasa guda daya, daukacin al'ummun gabobin biyu Sinawa ne, babu wanda zai iya canja alaka da asalinsu har abada, ban da haka, shugaba Xi ya bayyana cewa, ba zai yiyu a hana ci gaban alakar gabobin biyu ba, kana ci gaban kasa, da farfadowar al'umma, da ma dinkewar sassa biyu gu daya batu ne da zai gudana yadda ya kamata, lamarin da babu wanda zai iya hana shi. Wannan shi ne darasin da aka koya wajen bunkasar dangantakar dake tsakanin yankin Taiwan da babban yankin Sin har na tsawon shekaru 70, wanda kuma zai wayar da kanmu wajen warware batun Taiwan a nan gaba da ma cimma burin farfadowar al'ummar Sin.

A shekaru 40 da suka gabata, tattalin arzikin yankin Taiwan ya fi na babban yankin bunkasa sosai. Amma a yanzu, babban yankin kasar Sin ya zama kasa mafi girma ta biyu a duniya ta fuskar tattalin arziki, wadda kuma ta zama babbar aminiyar cinikayyar Taiwan, kasuwar shigo da kayayyakin Taiwan mafi girma, da ma wadda ta fi zuba yawan jari a yankin. Sassan biyu sun kara hadewa da juna, wanda ya amfana wa jama'a sosai. Daga watan Janairu zuwa Nuwamba na shekarar 2018, a karon farko jimillar cinikayya a tsakaninsu ta zarce dala biliyan 200, wadda ta karu da kashi 16% bisa a shekarar 2017. Yayin da yawan mazauna yankin Taiwan da suka zo babban yankin ya zarce miliyan 5.6, wanda ya karu da kashi 4% bisa na shekarar 2017. A waje daya kuma, kasashe da dama sun katse huldar diplomasiyya da ke tsakaninsu da yankin Taiwan, sa'an nan sun kulla ko farfado da huldar diplomasiyya tare da jamhuriyar jama'ar Sin. Akidar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya tana ta samun amincewar kasashen duniya.

Idan muka kwatanta da na shekaru 40 da suka wuce, za mu fahimci cewa, sharrudan dinkewar sassan biyu gu daya sun cika. Ya zama wajibi a bullo da wani sabon yunkurin siyasa wajen ciyar da batun gaba. Jawabin shugaba Xi ya dogara ne da yanayin ci gaban tarihi, da muradun al'ummar Sin, da ma burin jama'a, inda ya gabatar da matakai biyar, wadanda suka hada da hadin gwiwa don sa kaimi ga farfadowar al'ummar Sin da cimma burin kasancewar sassan biyu sun dunkule waje guda, da yin nazari kan shirin tsarin mulki biyu domin dinkewar sassan biyu gu daya lami lafiya, da tsayawa tsayin daka kan akidar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya da kiyaye makomar samun dinkewa lami lafiya, da inganta hadin kan sassan biyu domin aza harsashe mai inganci ga aikin dinkewar, da kara fahimtar 'yan uwa na sassan biyu domin su amince da wannan burin.

Wadannan matakai sun dace da manufar kwamitin tsakiya na JKS kan dangantakar da ke tsakanin sassan biyu, da ma sabon yanayin da ake ciki yanzu. Don haka za su zama babbar ka'idar kasar Sin wajen farfadowar al'ummar Sin da ma sa kaimi ga dinkewar kasa gu daya lami lafiya.

A cikin manufofin 5, an ce, Sinawa ba su nuna kiyayya ga juna ba, Sinawa za su taimakawa juna, kuma an yi kira da a sa kaimi ga kafa tsarin hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin gabobin biyu dake mashigin tekun Taiwan, da raya kasuwar gabobin biyu sun shaida sahihanci ga jama'ar yankin Taiwan, ana fatan jama'ar za su more damar da babban yankin kasar Sin ya samar domin kara bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima. An jaddada cewa, nasarar dinkuwar dukkan kasar Sin cikin lumana da manufar kasa daya tsarin mulki biyu ita ce hanya mafi dacewa wajen samun dinkuwar dukkan kasar. An yi kira ga jam'iyyu da bangarori daban daban na gabobin biyu da su zabi wakilansu tare da yin shawarwari da juna bisa tsarin demokuradiyya da kokarin bullo da matakan shimfida zaman lafiya da samun ci gaba cikin lumana a tsakanin gabobin biyu, wanda ya shaida cewa, iyalai su tattauna harkokinsu da kansu, su kuma yi shawarwari cikin adalci. Kana an jaddada cewa, Sin tana adawa da duk wani mataki na neman ware yankin Taiwan daga kasar Sin, kana Sin ba ta yi alkawarin kasa yin amfani da karfin tuwa ba, da daukar matakai bisa yanayin da ake ciki kan duk wani bangarorin waje da suka tsoma baki kan wannan batu da ma 'yan aware na yankin Taiwan, za kuma ta tsaya tsayin daka kan tabbatar da 'yancin kasar da cikakken yankunanta.

A cikin shekaru 40 da fara aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a cikin gida, kasar Sin ta shiga sabon lokaci na kusan cimma burin farfado da al'ummar kasar Sin a tarihi, kana ana samun cikakkun sharuda a kokarin samun dinkuwar dukkan kasar Sin cikin lumana. Game da wannan batu, kafofin watsa labaru na yankin Taiwan sun bayyana cewa, babban yankin kasar Sin ya samu ikon jagorancin raya dangantakar dake tsakanin gabobin biyu.

'Yan uwa za su warware matsalolinsu a karshe. A halin yanzu, Sinawa suna yin kokari wajen cimma burinsu, mazauna yankin Taiwan suna cikinsu, ya kamata dukkan Sinawa su hada kai don cimma burin inganta rayuwar al'umma mai wadata. Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana, akwai bukatar samun dinkuwar dukkan kasar Sin wajen samar da kyakkyawar makomar yankin Taiwan, farfadowar al'ummar dukkan kasar za ta amfanawa jama'ar yankin Taiwan. An fuskanci matsalar yankin Taiwan ne domin ba ya samun karfi sosai ba, tilas a kawo karshen wannan matsala idan aka yi nasarar farfadowar dukkan al'ummar kasar Sin.(Jamila Kande Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China