in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cika shekara daya da fara zirga-zirgar jirgin kasa tsakanin Habasha da Djibouti
2019-01-02 16:10:51 cri

Ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2019, rana ce ta cika shekara daya da fara zirga-zirgar layin dogon da ya hada birnin Addis Ababa na kasar Habasha da birnin Djibouti na kasar Djibouti dake gabashin Afirka. Wadanne irin sauye-sauye ne layin dogon ya kawo ga zaman rayuwar al'ummar kasashen? Kuma mene ne makomar layin dogon?

Da misalin karfe 8 na safiyar ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2019, a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, fasinjoji na shiga cikin jirgin kasa a tasha ta farko ta layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti wato tashar Labu. Wadannan fasinjojin ba za su damu da gajiyar doguwar tafiya cikin mota ba, kuma suna jin dadin zirga-zirga ta jirgin kasa daga Habasha zuwa Djibouti, wanda ya fara aikin jigilar fasinjoji a ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2018.

Tsawon layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti ya kai kilomita 752.7, wanda kuma saurin tafiyarsa zai iya kaiwa kilomita 120 a awa daya. Kamfanin CCECC, gami da kamfanin CREC na kasar Sin su ne suka yi aikin shimfida layin dogon, wanda ya hada fadar mulkin kasashen biyu wato Habasha da Djibouti. Layin dogon ya kuma zama irinsa na farko na zamani mai aiki da wutar lantarki da aka shimfida a nahiyar Afirka, wanda ya rage yawan lokutan da aka shafewa wajen zirga-zirga a kasa tsakanin Habasha da Djibouti daga mako daya na da, zuwa awoyi goma da 'yan kai. Har wa yau kuma, saboda tsadar tikitin jirgin sama da wahalar tafiya cikin mota, fasinjoji sun fi zabar jirgin kasa don yin zirga-zirga. Bisa alkaluman da aka yi, zuwa karshen shekara ta 2018, adadin yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti ya tasam ma dubu 130, al'amarin da ya saukakawa mazauna wurin yin zirga-zirga.

Adamu na daya daga cikin fasinjoji wadanda suka yi tafiye-tafiye na yau da kullum ta jirgin kasan, inda ya bayyana cewa:

"Layin dogon shi ne irinsa na farko na zamani da aka shimfida a nahiyar Afirka, abun dake da babbar ma'ana ga kasar Habasha, da ma nahiyar Afirka baki daya. Layin dogon ba ya taimakawa wajen rage matsin lambar da Habasha take fuskanta ta fannin sufuri kawai ba, har ma ya samar da babban alfanu ga 'ya'yanmu."

Baya ga samar da sauki ga zirga-zirgar fasinjojin, layin dogon shi ma na jigilar kayayyaki da hajoji tsakanin kasashen biyu. Wani jami'in kula da harkokin kasuwanni na kamfanin kiyayewa gami da kula da layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti, Li Shuangchong ya bayyana cewa, kafin kaddamar da shi a hukumance, tun a shekara ta 2016, bisa bukatar gwamnatin kasar Habasha, layin dogon ya fara aikin jigilar abincin gaggawa don tallafawa mutanen da bala'in ya shafa, sa'annan bayan da aka kaddamar da shi, layin dogon ya soma jigilar takin zamani, matakin da ya taimaka ga bunkasa ayyukan noma a kasar. Mista Li ya ce:

"Habasha kasa ce dake da yawan mutane, amma ba ta iya biyan bukatunta ta fannin abinci, har ma tana fuskantar babban matsin lamba wajen jigilar kayayyaki. Layin dogo mai saurin tafiya da muka gina musu, zai iya taimakawa gwamnatin Habasha wajen magance matsalar abinci. Har wa yau kuma, ayyukan gonan kasar na dogaro kan yanayi sosai, alal misali, dole ne a saka takin zamani a wani lokaci na musamman, shi ya sa ayyukan gona za su fuskanci babban matsin lamba a lokacin. Idan hakan ya faru, gwamnatin kasar za ta bukace mu, mu taimaka wajen yin jigilar takin zamani, kuma mun riga mun yi jigilar har ton 28483.95."

Habasha kasa ce ta biyu mafiya yawan al'umma a nahiyar Afirka, wadanda ke da babbar bukata ga kayayyaki iri daban-daban, kana rashin iya jigilar kayayyaki na haifar da tsaiko ga ci gaban tattalin arzikin kasar. Ita ma kasar Djibouti tana fatan raya tattalin arzikinta ta hanyar karfafa hadin-gwiwa tare da Habasha, kuma layin dogon ya zama tamkar wata gada tsakaninsu dake kawowa kasashen biyu moriya tare. Tun bayan da aka kaddamar da shi, ya zuwa yanzu, adadin yawan sundukan da aka yi jigilarsu ta layin dogon ya kai 44580, inda yankunan masana'antu dake yankin layin dogon suke kara bunkasa cikin sauri.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China