Rahoton ya yi nuni da cewa, tsakanin shekarar 2012 zuwa ta 2017, kasar Sin ta bayar da taimakon da ya kai kaso 22.5%, ga karuwar kayayyakin da ake shigo da su daga ketare a duniya baki daya.
Rahoton ya ce, bayan da Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ta yi ta kara shigo da kayayyaki daga ketare, musamman ma bayan da ta shiga kungiyar WTO a shekarar 2001, kayayyakin da take shigowa da su daga ketare sun yi ta karuwa cikin sauri. Daga shekarar 1978 zuwa ta 2017, yawan kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga ketare sun karu daga dala biliyan 10.9, zuwa biliyan 1841, adadin da ya ninka har sau 169, kuma kason kayayyakin da kasar ta shigo da su daga ketare sun karu daga kashi 0.93% zuwa 11.59% kwatankwacin kayayyakin da ake shigowa da su a duniya baki daya, lamarin da ya sa kasar Sin ta daga matsayinta daga na 23 a shekarar 1979 zuwa na biyu a shekarar 2017, wajen shigo da kayayyakin kasashen ketare. (Lubabatu)