in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar za ta hada kan kasashen da suka hada da Saudiyya wajen gudanar da atisayen soja
2019-01-02 11:09:29 cri
A jiya Talata, kakakin rundunar sojan kasar Masar ya bayar da sanarwa, inda ya ce, sojojin ruwan kasar sun isa kasar Saudiyya a wannan rana, domin hadin gwiwa da takwarorinsu na kasashen Saudiyya, da Jordan, da Yemen, da Djibouti da kuma Sudan, wajen gudanar da atisayen soja.

Sanarwar ta ce, burin da ake neman cimmawa a wannan atisayen soja shi ne, inganta kwarewar sojojin wajen gudanar da yaki na hadin gwiwa a kan teku. Rundunar sojojin Masar na kokarin bunkasa hulda da takwarorinta na kasashen da abin ya shafa, ta yadda za su tinkari kalubalen da suke fuskanta, da ma kiyaye tsaro da zaman lafiyar a shiyyar, kuma wannan atisayen soja wani mataki ne da aka dauka domin cimma wannan buri.

A cikin kusan shekara daya da ta gabata, Masar ta hada kan kasashen Amurka, da Faransa, da Ingila, da Italiya, da hadaddiyar daular Larabawa, da Bahrain da kuma Kuwait, wajen gudanar da atisayen soja, atisayen da ya shafi rundunar soja ta kasa da ruwa da kuma ta sama.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China