in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin wasu kasashe sun gabatar da sakwannin murnar sabuwar shekarar 2019
2019-01-02 11:07:04 cri
Kwanan baya, Shugabannin kasashen duniya da dama sun gabatar da sakwannin murnar sabuwar shekara ta 2019, inda suka nuna cewa, za mu tinkari nau'o'in kalubaloli da suke fuskanta cikin himma da kwazo, da inganta bunkasuwar kasashensu da kuma hadin gwiwar kasa da kasa, domin gina kyakkyawar makoma.

Cikin sakonsa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, akwai ayyuka da dama dake gaban kasar Rasha da take fatan kammalawa, wadanda suka shafi fannonin tattalin arziki, kimiyya da fasaha, ilmantarwa, da raya al'adu da dai sauransu.

Ita kuwa shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel cewa ta yi, a halin yanzu, kasar Jamus tana fuskantar kalubaloli da dama a fannonin sauyin yanayi, da aiwatar da harkokin tallafawa 'yan gudun hijira, da kuma yaki da 'yan ta'adda da dai sauransu.

A nata bangare kuma, firaministar kasar Burtaniya Theresa May, cewa ta yi tana fatan kasarta, za ta iya kafa wata hulda mai kyau da kasashen kungiyar Turai ta EU cikin shekarar 2019.

Shi kuwa firaministan kasar Australia Scott Morrison ya ce, cikin shekarar 2018 da ta wuce, tattalin arzikin kasar ya karu sosai, wanda ya ba da babban goyon baya ga kasar wajen gudanar da aikin kwaskwarima a fannin tallafawa al'ummar kasa.

Haka zalika, shi ma cikin sakonsa, shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya bayyana cewa, jam'iyya mai mulkin kasar, da gwamnatin sa, suna tsayawa tsayin daka kan hana yaduwar makaman nukiliya a duk fadin zirin Koriya. Ya kuma kara da cewa, a shirye yake ya sake yin shawarwari da shugaban kasar Amurka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China