in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya ta zargi wakilin MDD da shiga harkokin cikin gidan ta
2019-01-02 10:49:33 cri
Ministan ma'aikatar harkokin waje da hadin gwiwa da sassan duniya na kasar Somaliya, ya zargi wakilin musamman na babban magatakardar MDD game da kasar Nicholas Haysom, da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar.

Kalaman ministan sun zo ne bayan da wakilin MDDr ya bukaci mahukuntan Somalia, da su yi bayani game da ko tawagar da MDD ke marawa baya na da hannu cikin harbe masu zanga zanga a birnin Baidoa dake kudancin kasar a watan da ya gabata.

Mr. Haysom ya aike da wasika ga gwamnatin kasar, yana neman bayani game da harbin masu zanga-zangar, da kuma batun damke tsohon mataimakin shugaban kungiyar al-Shabab Mukhtar Robow, wanda shi ne babban dan hamayya, a zaben shugabancin kasar daga yankin kudu maso yammacin kasar.

Damke Robow dai ya haifar da dauki ba dadi tsakanin magoya bayansa da jami'an tsaron kasar, tsakanin ranekun 13 zuwa 15 ga watan Disamba, lamarin da ya sabbaba kisan mutane sama da 10.

Kawo yanzu dai Mr. Haysom bai mayar da martini game da zargin da gwamnatin Somalia ta yi masa ba. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China