in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Kara yin himma da kwazo domin "neman karin saurin ci gaban kasar Sin"
2019-01-01 14:18:53 cri

A ranar Litinin, 31 ga watan Disamban shekarar 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekarar 2019 ta babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG da shafukan intanet, inda ya nuna fatan alheri ga mazauna kasar Sin da na waje. A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jiping ya takaita ci gaban da kasar Sin ta samu a shekarar 2018, ya kuma bukaci kowanne Basine da ya ci gaba da yin kwazo da himma a sabuwar shekarar 2019. A waje daya, ya nuna sahihancin kasar Sin a kullum wajen tabbatar da zaman lafiyar duk duniya da kuma ci gaban ta baki daya. Wannan jawabi yana cike da alfaharin da al'ummar Sinawa take da shi ga ci gaban da ta samu sakamakon nuna himma da kwazo, har ma ya bayyana yadda Xi Jinping, shugaban wata babbar kasa yake tausayin al'ummarsa da ma duniya baki daya.

Kasar Sin ta samu sakamako na "al'ajabi" biyo bayan himma da kwazo

Shekarar 2018 shekara ce ta cika shekaru 40 da kaddamar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje a kasar Sin. A lokacin da ake nuna mamaki ga sakamakon kafa da kuma bunkasa cikakken tsarin masana'antu cikin goma-goman shekarun da suka gabata kawai maimakon daruruwan shekarun da wasu kasashe masu arziki suka yi amfani da su, a kan ambaci kalmar "himma da kwazo".

A cikin jawabai da dama da Xi Jinping ya bayar, ya kan nuna yabo ga ruhun "himma da kwazo" da Sinawa suke da shi. Alal misali, a yayin taron murnar cika shekaru 40 da kaddamar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga waje a kasar Sin, Xi Jinping ya yi alfahari cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu cikin shekaru 40 da suka gabata, sun faru ne saboda himma da kwazo da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da al'ummomin Sinawa suka yi bisa basira da karfinsu. Sannan a cikin jawabin murnar sabuwar shekarar 2019 da ya gabatar, Xi Jinping ya takaita ci gaban da kasar Sin ta samu a shekarar 2018 a fannonin tattalin arziki, kiyaye muhalli, inganta rayuwar al'umma da kirkiro sabbin fasahohin zamani da ayyukan kara yin gyare-gyare da bude kofa, ya kuma jaddada cewa, Sinawa sun yi namijin kokarin sun samun wadannan ci gaba a sabon zamanin da ake ciki. A wannan shekarar da ta gabata, kasar Sin ta "tsaya kan niyyarta ta samun ci gaba kamar yadda ya kamata", "kasashen duniya sun ga yadda kasar Sin ta yi gyare-gyare a gida da bude kofarta ga waje cikin sauri, har ma sun ga yadda kasar Sin take da niyyar kara yin gyare-gyare da bude kofarta ga waje har abada."

Yin kokari don cimma burin jama'a na jin dadin zaman rayuwa. Sinawa sun kara jin dadi da cimma burinsu ta hanyar yin kokari. A shekarar 2018, mutane miliyan 10 ne suka fita daga kangin talauci a kasar Sin, kana an rage farashin magungunan yaki da cutar daji guda 17 da shigar da su a jerin sunayen magungunan inshorar jinya, mutane miliyan 13 sun samu aiki a birane, kana an fara gina gidaje miliyan 5 da dubu 800 don rage matsalar gidajen kwana, kana mazaunan yankin Hong Kong, da Macau, da Taiwan sun samu takardun iznin zama a babban yankin kasar Sin, an kuma shigar da yankin Hong Kong a cikin tsarin jiragen kasa mafi sauri na kasar Sin, an gabatar da matakan yin kwaskwarima fiye da 100 da dai sauransu. Wadannan fasahohin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekara ta 2019 sun shaida cewa, an samu kyakkyawar rayuwa ta hanyar yin kokari, kuma dukkan Sinawa suna alfahari game da wannan batu.

Tunawa da maida hankali da nuna godiya su ne abubuwan dake cikin zuciya yayin da ake yin kokari.

Ko wane mutum na da burin da ya ke fatan cimmawa. Manyan fasahohin da aka samu a cikin shekaru 40 da fara aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a kasar Sin su ne sakamakon da aka samu ta hanyar kokarin da mutane da dama suka yi.

A cikin jawabin shugaba Xi Jinping na murnar sabuwar shekara ta 2019, ya zayyana wasu sunayen mutane, kamar masanin sararin samaniya da ya kirkiro babban madubin hangen-nesa Nan Rendong, sojoji mafi kwazo na kasar Sin Lin Junde da Zhang Chao da dai sauransu, shugaba Xi yana kiransu da sunan "mutane mafiya kwazo a sabon lokaci", ya kamata kowa da kowa ya yi koyi da su. Kana Xi Jinping ya tuna da jami'an yankuna masu talauci wadanda suka jagoranci jama'ar yankunan wajen yaki da talauci, yana fatan za su kula da lafiyar jikinsu. Haka kuma shugaba Xi ya waiwayi mutanen dake fama da matsaloli, yana fatan za su warware matsalolin zaman rayuwarsu. Shugaba Xi Jinping ya nuna godiya ga masu ba da hidimar jigilar kayayyaki, da masu tsabtace tituna, da direbobin tasi da sauransu, ya ce mutane ne masu samar da kyakkyawar rayuwa da dorewarta. Wadannan tunawa da maida hankali da nuna godiya sun shaida cewa, shugaba Xi Jinping yana kaunar jama'ar kasar sosai.

Hakika Xi Jinping shi kansa yana wakiltar daukacin ma'aikatan kasar Sin, wadanda ke matukar kokari kan aikinsu. A cikin shekarar da ta gabata, ya ziyarci yankin Liangshan na lardin Sichuan da birnin Jinan na lardin Shandong da birnin Fushun na lardin Liaoning da garin Qingyuan na lardin Guangdong da sauran wurare dake fadin kasar domin gudanar da rangadin aiki, haka kuma ya yi cudanya da shugabannin wasu kasashen duniya daga duk fannoni yayin da yake halartar ayyukan diplomasiyyar da aka shirya a nan kasar Sin da kuma yayin da ya ziyarci kasashen dake nahiyoyi biyar a fadin duniya. Tarin ayyukan da ya yi sun nuna mana cewa, shugaba Xi shugaban babbar kasa ne mai himma da kwazo wanda ke sauke nauyi dake wuyansa. Kana an lura cewa, kasar Sin tana gabatar da manufofinta yayin da kasashen duniya suke fuskantar kalubale tare, misali rage gibin dake tsakanin masu arziki da matalauta, da dakile matsalar kazantar muhalli da tafiyar hawainiyar karuwar tattalin arziki da sauransu, a sanadin haka, zumuncin dake tsakaninta da sauran kasashen duniya shi ma yana kara karfafa a kai a kai.

"Niyyar kasar Sin a fannoni biyu ba za ta canja ba" ya kuma nuna wa kasashen duniya niyyarta a matsayinta na babbar kasa

Shekara ta 2019, shekara ce ta cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ita ma muhimmiyar shekara ce ta kafa zaman al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni, yanzu ra'ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra'ayin gudanar da cinikayya bisa bangare guda suna ci gaba da karuwa, lamarin da ya kawo rashin tabbas ga ci gaban kasar Sin da ma duniya baki daya, a don haka nuna kwazo da himma a ko da yaushe shi ne mafi muhimmanci ga kasar Sin, wadda ta kasance kasa mai tasowa mafi girma a duniya.

A 'yan kwanakin baya, kasar Sin ta tsara wani shiri kan yadda za a gudanar da ayyukan raya tattalin arziki da ci gaban al'umma a bana, inda ba ma kawai ta jaddada aniyarta ta kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare ba, hatta ma ta nanata hasashenta na lura da jama'a, wato za ta kyautata zaman rayuwar jama'arta ta hanyar kara yin kwaskwarima daga dukkan fannoni da kara bude kofarta ga waje. Game da wannan, shugaba Xi ya yi nuni cikin sakonsa na sabuwar shekara cewa, a shekara mai zuwa, za a samu damammaki da ma kalubaloli, don haka ya kamata kowa da kowa ya kara zage damtse domin samar da damammaki ga kamfanoni ta hanyar rage harajin da za su biya. Ban da haka za a kara himma da kwazo domin fitar da mutane sama da miliyan 100 daga yanayin na kangin talauci da suke ciki. Haka zakila, shugaba Xi ya jaddada cewa, "Duk da sauye-sauyen da duniya ke fuskanta, aniyar kasar Sin ta kiyaye 'yancin da ma tsaron ta ba za ta canza ba, aniyarta ta kiyaye zaman lafiyar duniya da kokarin samun ci gaban duniya gaba daya ita ma ba za ta canza ba". Wadannan aniya biyu sun shaida babban burin kasar Sin a matsayinta na babbar kasa, kana da babban burin Xi Jinping na bayar da gudummawa ga zaman lafiya da ci gaban bil Adama a matsayinsa na shugaban babbar kasa.

A cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta samu saurin ci gaba ta hanyar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, da neman samun bunkasa bisa karfin kanta, da ma yin kokari ba tare da kasala ba, har ma ta cimma wasu nasarori marasa yiwuwa a ganin wasu. A shekaru 40 masu zuwa ko fiye, kasar Sin za ta kara saurin ci gabanta bisa namijin kokarin da za ta yi, domin cimma burin farfadowar al'ummar Sin, da sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da ma raya makomar bil Adama ta bai daya. Mun riga mun shiga sabuwar shekara, jama'ar Sin na yi mata maraba cike da imani da fatan alheri.(Sanusi Zainab Jamila Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China