in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya gabatar da sakon murnar sabuwar shekara ta 2019
2018-12-31 19:12:01 cri


A gabannin sabuwar shekarar dake tafe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da sakon taya murnar shiga sabuwar shekara ta 2019, ta babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin wato CMG da kuma kafar intanet, inda ya bayyana cewa,

Ya ku abokai:

Barka da sabuwar shekara! Har kullum lokaci na gudana cikin sauri, shekara ta 2019 tana zuwa, don haka ina taya ku murnar shiga sabuwar shekara, tare kuma da isar da fatan alheri a gare ku daga nan birnin Beijing.

Mun yi kokari matuka a shekarar 2018, haka kuma mun samu sakamako mai gamsarwa, a cikin wannan shekarar da za ta wuce, mun dakile matsaloli da kalubaloli daban daban, domin cimma burin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci, tare kuma da tafiyar da tattalin arzikin kasar cikin kwanciyar hankali, ta hanyar da ta dace. Kana mun samu sakamako mai faranta rai a fannoni daban daban, misali kiyaye muhalli da kyautata rayuwar al'ummar kasar. Ban da haka, mun samu ci gaba a bayyane a yankunan hadin gwiwar biranen Beijing, da Tianjin, da ma lardin Hebei, da yankunan dake gabar kogin Yangtse, da ma yankunan hadin gwiwa dake tsakanin lardin Guangdong da yankunan musamman na Hong Kong da Macau. Yayin da na yi rangadin aiki a wurare dake fadin kasar, na lura cewa, muhallin yankunan dake gabar kogin Yangtse yana kara kyautatuwa, har ana iya ganin girbin shinkafa a yankin Jiansanjiang da ke lardin Helongjiang. A yankin Qianhai na birnin Shenzhen na lardin Guangdong da kuma yankin Zhangjiang na birnin Shanghai, ana iya ganin al'ummar biranen suna cike da kuzari domin ciyar da tattalin arzikinsu gaba yadda ya kamata, kana abu mafi burge mu shi ne babbar gadar da ta hada yankin Hong Kong da birnin Zhuhai, da kuma yankin Macau ta fara aiki lami lafiya, duk wadannan sakamakon da aka samu sun shaida mana cewa, al'ummomin kabilu daban daban na fadin kasar Sin, suna kwazo da himma kan ayyukan da suke gudana.

A cikin shekarar 2018, masu aikin kimiyyar kasar su ma sun yi kokari matuka har sun samu babban sakamakon da zai sauya yanayin da kasar ke ciki, misali an harba tauraron dan Adam na Chang'e-4 cikin nasara, babban jirgin ruwa mai saukar jiragen saman yaki na biyu ya yi gwajin tafiya a kan teku, babban jirgin sama kirar kasar Sin da ake yin amfani da shi kan kasa ko ruwa ya tashi sama a karo na farko, fasahar na'urar tantance bayanai da wurare ta GPS samfurin Beidou ta kai sahun gaba a fadin duniya, a don haka ina nuna girmamawa ga kowanen ma'aikacin kimiyya da injiniya da ma'aikacin kera na'urorin.

A cikin shekarar, gwamnatin kasar Sin ita ma ta samu babban sakamako a fannin yaki da talauci, karin gundumomi da yawansu ya kai 125 sun fice daga sunayen gundumomin dake fama da talauci, har adadin manoman kauyuka wajen miliyan 10 sun kubutar da kansu daga kangin talauci. Kana farashin magungunan sha guda 17 masu amfani wajen jiyyar ciwon kansa ya ragu, kuma an shigar da su cikin jerin sunayen magungunan sha iri na inshorar jinya ta kasar, ta haka matsalar fadawar masu fama da ciwon cikin mawuyacin halin talauci ya kau. Ni kai na ina begen jami'an da suke gudanar da aikin yaki da talauci a wurare daban daban na fadin kasar, musamman ma darektocin kwamitin JKS ko jami'ai sama da miliyan 2 da dubu 800 wadanda ke aiki a kauyuka, ina fatan za su kula da lafiyar jikinsu sosai.

Har kullum ina tunanin manoman dake fama da talauci, na taba kallon iyalai guda biyu na kabilar Yi wato Jihaoyeqiu da Jielie'e'amu a kauyen Sanhe na yankin Liangshan na lardin Sichuan. Kana na taba yin hira da iyalin Zhao Shunli a kauyen Sanjianxi na birnin Jinan dake lardin Shandong. A unguwar Donghuayuan ta birnin Fushun na lardin Liaoning, na taba zuwa gidan Chen Yufang domin kara fahimtar yanayin da suke ciki bayan kaurarsu daga wurare daban domin kaucewa aukuwar hadari. A kauyen Lianzhang na garin Qingyuan na lardin Guangdong, na taba tattaunawa da manomi Lu Yihe kan yadda za a yi yaki da talauci. Har yanzu ban taba mantawa da fuskokinsu masu sahihanci ba, a gabannin zuwan sabuwar shekara, ina taya sumurna da fatan alheri, ina fatan rayuwarsu za ta kyautata sannu a hankali.

A cikin shekarar, mun shirya gagarumin bikin taya murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, mun kuma yin kwaskwarima kan tsarin hukumomin gwamnatin kasar da na jam'iyyar kwaminis ta kasar, har ma mun fitar da matakai sama da 100, kana mun shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar daga ketare na kasa da kasa karo na farko, haka kuma mun fara gina yankin gwajin cinikayya maras shinge a lardin Hainan. A bayyane take cewa, al'ummomin kasashen duniya sun lura da niyyar gwamnatin kasar Sin ta kara habaka yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, ko shakka babu ba za mu daina kokarinmu na yin gyare-gyare ba, haka kuma za mu kara bude kofa ga kasashen waje.

Na lura cewa, ya zuwa bana, yawancin daliban da suka shiga jami'a a shekarar 1978, wato lokacin da aka maido da jarrabawar shiga jami'a a kasar Sin sun riga sun yi ritaya, samari wadanda aka haife su bayan shekarar 2000 sun shiga jami'a domin yin karatu a ciki. Kana manoma sama da miliyan 100 sun fara rayuwarsu a birane a kai a kai, baya ga yadda wasu miliyan 13 sun riga sun samu aikin yi a garuruwa. Domin warware matsalar rashin cikakken muhalli wajen rayuwa da wasu mutane ke fuskanta a birane, gwamnati ta kaddamar da aikin gina gidajen kwana kusan miliyan 5 da dubu 800 gare su. Ban da haka mazaunan Hong Kong da Macau da Taiwan da yawan gaske, sun samu iznin sauka a babban yankin kasar Sin, har ma an hada Hong Kong da babban yankin kasar da layin dogo mai saurin tafiya. Muna cikin wata kasa mai cike da kuzari da wadata, inda al'ummominta suke hada kai matuka, kowa da kowa muna yin kokari na cimma burinmu.

A nan bari na gabatar muku wasu sunaye, na jami'in kimiyya Nan Rendong, ga sojoji jarumai Lin Junde da Zhang Chao, ga Wang Jicai wanda ya dade yana aikin kiyaye tsaron tsibiri har na tsawon shekaru 32, ga ma'aikata wadanda suka sadaukar da rayuka yayin aiki Huang Qun da Song Yuecai da Jiang Kaibin, da sauran su, muna mayar da su a matsayin mutane mafiya samun karbuwa a sabon zamanin da ake ciki, ba za mu manta da su ba har abada.

A shekarar, sabbin abokai ko tsoffin abokai da yawan gaske sun zo nan kasar Sin, domin halartar taron shekara shekara na dandalin Asiya na Bo'ao, da taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai na Qingdao, da taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing, da sauran harkokin diplomasiyyar da aka shirya a kasar Sin, inda muka gabatar da manufofin kasar Sin. Ni da abokaina mun je nahiyoyi biyar domin halartar muhimman ayyukan diplomasiyyar da aka shirya, tare kuma da tattaunawa da shugabannin kasashe daban daban daga duk fannoni, da haka mun kara inganta zumunci da fahimtar juna dake tsakaninmu.

A shekarar 2019 dake tafe, za mu shirya gagarumin biki domin taya murnar cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin. Duk da cewa, mun sha wahala a cikin wadannan shekaru 70, amma mun samu ci gaba bisa dogaro da al'ummar kasar, wadanda suke nuna wa al'ummomin kasashen duniya nagartattun halayensu wajen dogaron kansu karfinsu. A kan hanyar da za mu bi a nan gaba, za mu ci gaba da yin kokari bisa goyon bayan al'ummar kasa, domin ciyar da babban sha'aninmu na raya kasa gaba yadda ya kamata.

A shekarar 2019, za mu samu damammaki, haka kuma za mu fuskanci kalubale, a don haka ya dace mu yi kokari tare domin samar da damammaki ga kamfanoni ta hanyar rage harajin da za su biya, kana mu girmama kwararru a bangarori daban daban a fadin kasar, domin su kara taka rawarsu a fannin yin kirkire-kirkire. Ban da haka ya kamata mu kara mai da hankali kan muradun jami'an dake aiki a hukumomin gwamnati na kananan wuraren kasar, ta yadda za su kara nuna kwazo da himma kan aikinsu a yau da kullum. Haka zalika, za mu ci gaba da yin kokari domin samar da wadata ga mutane sama da miliyan 10, wadanda ke fama da kangin talauci, haka kuma za mu kara kula da sojojin da suka yi ritaya daga rundunar mu, saboda sun taba taka rawar gani wajen kiyaye tsaron kasar. Lallai, a wannan lokaci, masu aikin jigilar kayayyaki cikin sauri, da masu aikin shara kan hanya, da direbobin tasi, da sauran ma'aikata dubu gomai suna aiki, shi ya sa nake yi musu godiya, mun gode.

A halin da ake ciki yanzu, duk da cewa muna fama da manyan sauye-sauye a fadin duniya, amma niyyarmu ta kiyaye ikon mulkin kasa da tsaron kasa ba za ta canja ba, haka kuma niyyarmu ta kiyaye zaman lafiyar duniya da ingiza ci gaban duniya gaba daya ba za ta canja ba. Za mu ci gaba da aiwatar da shawarar "Ziri daya da Hanya daya" da manufar raya kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya, a kokarin gina duniya mai wadata ga daukacin bil Adam baki daya.

Za a ji karar agogon zuwan sabuwar shekara ba da jimawa ba, sai mu jira tare da imani domin taryen zuwan shekara ta 2019.

Fatan alheri ga kasar Sin! Fatan alheri ga duniya!

Mun gode! (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China