in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CMG: Muhimman labarai 10 kasa da kasa na shekarar 2018
2018-12-31 17:44:34 cri
Yayin da muke ban kwana da shekarar 2018, shekarar dake cike da labarun abubuwa masu daukar hankali da dama, ba za mu iya mantawa da wasu muhimman batutuwa da suka wakana a shekarar ba. Ga misali an ga yadda aka rika samun takun saka tsakanin wasu manyan sassa, da zaman tankiya a wasu yankuna, tare da sa-in-sa a fannin tattalin arziki. Mun ga yadda aki'du biyu suka rika nuna tasirin su – Aki'dar dunkulewar duniya da ta neman karbuwa ga kowa – wadanda suka rika karo da juna; Mun ga ci gaba mai armashi a matsayin gajiyar yakin cacar baka da aka samu; Mun ga munanan abubuwa da suka faru sakamakon sauyin yanayi; Mun ga ci gaba mai gamsarwa a zango na hudu na ci gaban masana'antu na wannan karni…

Gungun kafafen watsa labarai na kasar Sin ko CMG, ya zabi labarai 10 mafiya jan hankali a wannan shekara, wadanda suka kunshi waiwaye game da lokuta masu kayatarwa, da masu sosa zuciya, wadanda za a ci gaba da tunawa da su a cikin shekara mai zuwa.

1. Sin ta gudanar da taron baje koli na duniya irin sa na farko

A watan Nuwambar shekarar ta 2018 ne kasar Sin ta gudanar da taron baje koli na kayayyakin da ake shigowa kasar irinsa na farko a birnin Shanghai, yayin da ake tsaka da hali na rashin tabbas, game da yanayin tattalin arzikin duniya, wanda janyewar Amurka daga tsarin cinikayya na sassa daban daban ya yi wa matukar tasiri. Baje kolin na kwanaki 5 mai lakabin CIIE, wanda kuma ya haifar da cinikayyar da za ta kai ta dalar Amurka biliyan 57.8, ya dora wani dan ba, game da burin kasar Sin na fadada aiwatar da manufar kara bude kofar ta ga kasashen waje. Kuma hakan wani tagomashi ne ga kasar dake matsayin babban karfi mai bunkasa tattalin arzikin nahiyar Asiya da duniya baki daya.

2. Manufar "ziri daya da hanya daya" ta sake fadada

Manufar "ziri daya da hanya daya ko BRI" a takaice, ta shiga shekara ta biyar a shekarar 2018. Taro na biyu na ministocin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka da Karebiya, da ya gudana a birnin Santiago na kasar Chile a ranar 22 ga watan Janairu, wanda ya haifar da fitar da sanarwar BRI, wadda ta tabbatar da fadadar wannan babbar manufa zuwa Latin Amurka. A yayin taron dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da nahiyar Afirka da ya gudana a watan Satumbar shekarar ta 2018 a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da kudurori 8 da aka sanya gaba karkashin inuwar dandalin tare da kasashen na Afirka. A watan Nuwamba, taron baje koli na CIIE, ya tattara kamfanonin waje sama da 3,000, ciki hadda sama da 1,000 daga kasashe 58, wadanda suke cikin shawarar "ziri daya da hanya daya".

Kara kyautata alaka da Japan ya haifar da fadada hadin gwiwar hada hadar cinikayya da tsagi na uku, karkashin manufar "ziri daya da hanya daya". A daya hannun kuma, an kafa sabon tsarin inganta cinikayya bisa amfani da na'urori masu kwakwalwa a hanyar Siliki, ta yadda kamfanoni masu hada hada ta yanar gizo kamar Alibaba, suka fara hada hada karkashin wannan dadaddiyar hanya.

Ci gaban da aka samu ta hanyar hadin gwiwa da babban yankin Mekong, da sauran kasashen gabas ta tsakiya ya karfafa gwiwarmu wajen bunkasa shawarar "ziri daya da hanya daya".

3. Baya ga rikicin Syria an sha fama da yanayin zaman dar dar a gabas ta tsakiya

Yakin kasar Syria ya ci gaba da wanzuwa, inda a shekarar 2018 ya kai ga shekara ta Bakwai, inda tashe-tashen hankula suka jefa dubban 'yan kasar cikin mawuyacin hali. Sakamakon shigar kasashe da dama cikin wannan batu, yanayin ya kyautatu a shekarar ta 2018 – Gwamnatin kasar ta amshe iko da yankunan dake karkashin ikon 'yan tawaye, ta hanyar kaddamar da hare-hare masu yawa. Kasashen Turkiyya da Rasha sun jagoranci kafa yankin da aka haramta daukar matakan soji a cikinsa. Yayin da yakin kasar ke ci gaba, miliyoyin al'ummar Syria, ciki hadda yara kanana, na fuskantar barazanar kisa. A wannan shekara, an fuskanci yanayi na matsi a wasu kasashen na daban, da yankunan dake gabas ta tsakiya. Tashin hankali mafi tsanani tsakanin Falasdinawa da dakarun Isra'ila na baya bayan nan ya hallaka rayuka kusan 3,000. Kaza lika rashin jituwa tsakanin masarautar Saudiyya da kasar Turkiyya ya sauya wani sabon salo. A daya hannun kuma, Qatar ta fuskanci matsi da mayar da ita saniyar ware, sakamakon yanayin da fanninta na diflomasiyya ya shiga tun daga watan Yuni na shekarar 2017.

4. An samu sassauci a zirin Koriya sakamakon shiga tsakani na wasu sassa

Daya daga manyan abubuwan mamaki da suka wakana a shekarar 2018, shi ne kyautatuwar yanayi a zirin Koriya. Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un ya yi rawar gani a fannin diflomasiyya, inda ya nuna basira da karfin hali sama da na shekarunsa. A shekarar ya gana da shugaba Xi Jinping har karo uku cikin watanni uku, kana ya gana da shugaban Koriya ta kudu Moon Jae-in sau uku. Shugaba Kim da takwaransa na Amurka Donald Trump, sun gaisa hannu da hannu yayin wata ganawar da suka yi a kasar Singapore.

Kasar Sin ta shiga tsakani wajen wanzar da zaman lafiya tsakanin Koriya ta arewa da ta kudu, inda har shugaba Moon na Koriya ta kudu ya farfado da manufar "Sunshine", kana cikin wani salon ba kasafai ba, shugaba Trump na Amurka ya tattauna da Pyongyang, wanda hakan ya haifar da sakamako mai gamsarwa. To sai dai kuma, har yanzu ana iya cewa da sauran riba a kaba.

5. Yakin cinikayya na Amurka ya sanya duniya cikin damuwa, ko da yake sassan kasa da kasa sun ci gaba da hadin gwiwa da juna

A ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2018 ne shugaban Amurka Donald Trump, ya gabatar da sabon tsari na karin harajin da kasarsa za ta rika karba daga kayan karafa da sanholo, wanda ya haifar da kara harajin kayayyakin da kasar ke shigarwa cikin kasar Sin. Ba tara da jinkiri ba wannan yanayi na dambarwar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ya yadu zuwa sauran sassan duniya, ciki hadda yankunan Turai da Afirka. Manufar ba da kariya ga cinikayya ta Amurka – wadda a baya ita ce uwa ga manufar cudanyar cinikayya tsakanin dukkanin sassa– ta sanya hada hadar cinikayya cikin wani yanayi na ni-'ya-su, wanda hakan ya yi matukar tasiri ga sauran sassan duniya. Shugaba Trump ya dage kan manufar sa ta "Amurka gaban komai", duk da mummunan tasirin da hakan ya yi ga ci gaban duniya baki daya kawo farkon watan Disamba, lokacin da kasashen duniya biyu mafiya karfin tattalin arziki suka amince da dakatar da karawa juna haraji cikin kwanaki 90, yayin shawarar da aka yanke a gefen taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 wanda ya gudana a birnin Buenos Aires.

6. Karyewar yarjejeniyar INF ta jefa Turai cikin wani hali

A watan Oktoba na shekarar ta 2018, shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da aniyar gwamnatinsa, ta janyewa daga yarjejeniyar dakatar da kera matsakaitan makaman kare dangi ko INF a takaice, yarjejeniyar da Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet suka sanyawa hannu a shekarar 1987. Bisa tsarin, Amurka za ta aiwatar da janyewa daga yarjejeniyar ne cikin watanni shida. Karkashin yarjejeniyar dai an dakile shigar matsakaitan makaman kare dangi cikin yankunan Turai tsawon gwamman shekaru, to sai dai kuma janyewar da shugaba Trump ya ayyana, ta sanya kawayen Amurka dake kungiyar tsaro ta NATO cikin wani hali na tsaka mai wuya. A hannu guda kuma sauran sassan duniya su ma na fargabar abun da ka iya biyo baya, na gasar kera makaman kare dangi tsakanin manyan kasashen duniya.

7. Birtaniya na kan hanyar fita daga tarayyar Turai duk da kalubale daban daban da ake fuskanta

Game da ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai ta EU kuwa, firaminista Theresa May, ta sha matsin lamba daga sassa daban daban na 'yan adawa. Kawo yanzu, akwai rabuwar kawuna tsakanin 'yan majalissarta, wanda hakan ya kai ga murabus na sakatare mai lura da ficewar kasar daga EU a watan Nuwambar da ya shude. Idan har manufar ficewar kasar Birtaniya ta gaza samun goyon baya yadda ya kamata, to ko shakka babu kasar na iya fita daga tarayyar ta Turai ta hanya mafi wahala, wadda ka iya lahanta harkokin cinikayya, da haifar da rashin jituwa game da batun kan iyakoki, da halin rashin tabbas game da makomar zama dan kasa, da ta ayyukan yi, da ma zamantakewar al'ummar kasar dake zaune a kasashen waje.

8. Rashin tabbas a kasuwar danyen mai na iya kassara tasirin dalar Amurka

A wannan shekara ta 2018, an fuskanci hali na rashin tabbas a kasuwar danyen mai, wanda hakan ya haifar da damuwa a fannin makamashi tsakanin kasa da kasa, yayin da farashin danyen mai ke ci gaba da faduwa. Yayin da manyan kasashe masu karfi a fannin fitar da mai kamar su masarautar Saudiyya da Rasha suka rage yawan mai da suke fitarwa kasuwanni domin dakile yawaitar mai a kasuwa, Amurka ta sha gaban su, inda ta kasance kasa ta farko mafi fitar da danyen mai a duniya. Wanda hakan ya sanya ta karya farashin sakamakon yawa da ya yi a kasuwa.

9. Duniya na fuskantar mummunan tasirin sauyin yanayi

Mummunan tasirin sauyin yanayi ya haifarwa duniya asarar dalar Amurka biliyan 100, baya ga dubban rayukan al'umma da suka salwanta sakamakon hakan a shekarar ta 2018. A watan Agusta kasar India ta fuskanci yanayin ambaliyar ruwa mafi muni a dukkanin wannan karni, ibtila'in da ya hallaka rayukan mutane 1,400, baya ga wasu miliyoyin mutane da suka rasa muhallansu.

Sauyin yanayi ya haifar da ambaliyar ruwa ta yanayin zafi a kasar Japan, da guguwa mai karfi da ta ratsa yankunan Turai, da iska mai karfi da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya shafi wasu yankunan Amurka da Karebiyan a karshen lokacin bazara, da wutar daji da ta mamayi California, da kanfar ruwa ko fari da ya aukawa kasar Australia, dukkanin wadannan na nuni ga irin karfin da bala'u ke haddasawa, ko a ce mummunan sakamako na sauyin yanayi.

Duk da cewa Amurka ta janye daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, da yawa daga kasashe masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar na ci gaba da mara mata baya. Yayin taron baya bayan nan game da sauyin yanayi na MDD da ya gudana a birnin Katowice na kasar Poland, kusan wakilan kasashe 14,000 da suka kunshi ministoci, da masu shiga tsakani, da jami'ai daban daban daga kasashe da yankuna 195 ne suka cimma matsaya game da yadda za a aiwatar da yarjejeniyar ta Paris.

10. Fasahar kwaikwayar tunanin bil Adama na samun ci gaba

A duniyar yau fasahar kwaikwayar tunanin bil Adama a na'urori masu kwakwalwa ta wuce tunani ko wasan kwaikwayo. Domin kuwa a yanzu na'urori masu kwakwalwa sun fara shiga sassan saukakawa, da inganta rayuwar jama'ar duniya, ciki hadda fannin gano masu laifi. Ga misali irin wannan fasaha an yi amfani da ita, wajen gano wani mai laifi dake cikin dandazon mutane mahalarta wani taron kade kade a kasar Sin, kana an yi amfani da ita wajen hango wani wawakeken rami a duniyar wata.

A watan Satumba kuma na shekarar ta 2018, an gudanar da babban taron kasa da kasa game da fasahar kwaikwayar tunanin bil Adama, wanda aka yiwa take da "Sabon zamani wanda fasahar kwaikwayar tunanin bil Adama ta karfafa zuwansa," taron da ya gudana a birnin Shanghai.

Akwai kyakkyawan fata game da irin gajiya da za a ci daga wannan fasaha, sai dai kuma dole a yi taka-tsan-tsan duba da yadda mota mai tuka kanta da kanta, ta hallaka wani mutum da ya shiga gwajin da aka yi da ita. Duk da cewa har yanzu kalmar kwaikwayon tunanin bil Adama tamkar tatsuniya ce ga wasu masana'antu, a hannu guda akwai dama mai fadi ta raya sashen, da kuma cin gajiya daga gare shi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China