in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya gabatar da sakon murnar sabuwar shekara ta 2019
2018-12-31 19:09:43 cri

A gabannin sabuwar shekarar 2019, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da sakon murnar zuwan sabuwar shekara, inda ya isar da fatan alheri ga kowa da kowa.

Xi ya bayyana cewa, a shekarar 2018, mun yi kokari matuka a shekarar 2018, haka kuma mun samu sakamako mai gamsarwa, a cikin wannan shekarar da za ta wuce, mun dakile matsaloli da kalubaloli daban daban, domin cimma burin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci, masu aikin kimiyyar kasar su ma sun yi kokari matuka har sun samu babban sakamakon da zai sauya yanayin da kasar ke ciki, gwamnatin kasar Sin ita ma ta samu babban sakamako a fannin yaki da talauci, karin gundumomi da yawansu ya kai 125 sun fice daga sunayen gundumomin dake fama da talauci, har adadin manoman kauyuka wajen miliyan 10 sun kubutar da kansu daga kangin talauci. Mun shirya gagarumin bikin taya murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, mun kuma yin kwaskwarima kan tsarin hukumomin gwamnatin kasar da na jam'iyyar kwaminis ta kasar, har ma mun fitar da matakai sama da 100, kana mun shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar daga ketare na kasa da kasa karo na farko, haka kuma mun fara gina yankin gwajin cinikayya maras shinge a lardin Hainan. A bayyane take cewa, al'ummomin kasashen duniya sun lura da niyyar gwamnatin kasar Sin ta kara habaka yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare. Mun shirya muhimman ayyukan diplomasiyya da dama, tare kuma da tattauna da shugabannin kasashe daban daban daga duk fannoni, da haka mun kara inganta zumunci da fahimtar juna dake tsakaninmu.

Ya kara da cewa, dalilin da ya sa a samu sakamakon haka shi ne domin al'ummomin kasar Sin sun yi kokarin matuka, a don haka ya nuna girmamawa da fatan alheri ga daukacin al'ummomin kabilu daban daban na fadin kasar.

Shugaba Xi yana mai cewa, a shekarar 2019 dake tafe, za mu shirya gagarumin biki domin taya murnar cika shekaru 70 da kafa Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin, inda ya jaddada cewa, goyon bayan al'ummomin kasar Sin ya fi muhimmanci ne yayin da gwamnatin kasar ke kokarin raya kasa, a don haka JKS za ta ci gaba da yin kokari bisa goyon bayan al'ummar kasa, domin ciyar da babban sha'aninmu na raya kasa gaba yadda ya kamata.

A cikin sakon, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, duk da cewa muna fama da manyan sauye-sauye a fadin duniya, amma niyyarmu ta kiyaye ikon mulkin kasa da tsaron kasa ba za ta canja ba, haka kuma niyyarmu ta kiyaye zaman lafiyar duniya da ingiza ci gaban duniya gaba daya ba za ta canja ba. Za mu ci gaba da aiwatar da shawarar "Ziri daya da Hanya daya" da manufar raya kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya, a kokarin gina duniya mai wadata ga daukacin bil Adam baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China