Manazarta a birnin Beijing na kasar Sin sun yi nuni da cewa, hadin gwiwa zai kawo moriya, yayin da abin da rikici zai kawo sai hasara, wannan su ne darusan da aka samu a cikin shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka. Don haka ya kamata kasashen biyu su kara yin mu'amala da hadin gwiwa a fannoni daban daban, da girmama moriyar juna, da kokarin raya dangantakar dake tsakaninsu bisa tushen hadin gwiwa da zaman lafiya, yadda kasashen biyu da ma duniya baki daya za su amfana.
Jaridar The Wall Street Journal ta labarta cewa, shugabannin kasashen biyu sun yi mu'amala sosai, da yin shawarwari kan cinikayya a tsakaninsu yadda ya kamata, wanda ya sanya imani ga kasuwar hannayen jari ta kasar Amurka. Kamfanin dillancin labaru na Bloomberg yana ganin cewa, wayar da shugabannin kasashen biyu suka bugawa juna ta shaida cewa, shugabannin kasashen biyu sun amince da ci gaban da aka samu a shawarwarin cinikayya a tsakaninsu. Labarin ya kara da cewa, an samu canji kan yanayin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, a don haka yana da muhimmanci sosai da kasashen biyu su raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu. (Zainab)