in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Tianjin zai kara karfafa alaka da kasashen Afirka
2018-12-31 15:26:32 cri
Gwamnatin birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin ta bullo da wani shiri da nufin karfafa alaka da kasashen Afirka cikin shekaru uku da ke tafe.

Bisa wannan tsari, yankin zai karfafawa kamfanoninsa da dama gwiwar zuba jari da kuma bude masana'antu a kasashen na Afirka, ciki har da masana'antar sarrafa tumatur a kasar Ghana, da na hako zinare a Sudan da aikin hako tagulla da dalma a Zambia. Baya da wasu ayyukan zuba jari da ake nazari a kansu a nahiyar ta Afirka.

Bugu da kari, gwamnati ta karfafawa kamfanonin yankin gwiwar zuba jari a bangaren gina muhimman ababan more rayuwa a Afirka da kuma yadda kamfanonin sufurin jiragen sama za su fara zuwa kasashen Afirka kai tsaye. Yanzu haka aikin gina cibiyar kasuwanci da baje kolin kayayyakin kasar Uganda a Tianjin ya yi nisa, gami da bikin baje kolin kayayyakin yankin kan yadda za su rika shiga kasashen Afirka.

A bangaren musayar al'adu kuwa, an karfafawa kwalejojin koyon sana'o'i gwiwar bude wuraren koyon sana'o'i a kasashe kamar su Djibouti da Masar. Birnin na Tianjin zai kuma ci gaba da horas da dalibai daga kasashen Habasha da Equatorial Guinea da Mauritius da Najeriya da Tanzaniya kan fasahohi.

Haka kuma za a taimakawa makarantun koyar da aikin likitanci yadda za su gina cibiyoyin nazarin magungunan gargajiyar kasar Sin da gudanar bincike game da cututtukan da ake dauka a kasashen Afirka. (Ibrahim ayaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China