in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Rasha da Turkiyya za su ci gaba da aiki a Syria bayan ficewar dakarun Amurka
2018-12-30 16:35:43 cri

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya sanar a jiya Asabar cewa, sojojin kasashen Rasha da Turkiyya za su ci gaba da aikin murkushe 'yan ta'adda a Syria, da zarar Amurka ta janye dakarunta daga kasar.

Ya yi wannan tsokaci ne a taron manema labarai, bayan wata tattaunawa da ya halarta da takwaransa na kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu, da ministocin tsaro da manyan jami'an hukumar tattara bayanan sirri na kasashen biyu.

Bangarorin sun amince za su ci gaba da yin aiki tare karkashin kudurin kwamitin sulhun MDD mai lamba 2254, wanda ya kunshi mutunta ikon mallakar yankunan kasar Syria ba tare da gindaya wasu sharruda ba, in ji Lavrov.

Sun kuma bayyana wasu muhimman matakan da za su dauka, wadanda za su karfafa aikin hadin gwiwa, da samar da wani yanayin da za'a baiwa 'yan gudun hijirar Syriar damar komawa gidajensu, in ji shi.

Cavusoglu ya ce, bangarorin biyu sun kuma tattauna game da matakan da za'a bi wajen aiwatar da yarjejeniyar kafa wata cibiyar kawar da sansanonin sojoji a lardin Idlib dake arewa maso yammacin kasar ta Syria.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China