in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara zaben shugaban kasa a DRC
2018-12-30 16:11:00 cri

Masu jefa kuri'a a jamhuriyar demokradiyyar Kongo DRC sun fara jefa kuri'unsu a yau Lahadi, a wani muhimmin zaben da ake sa ran zai samar da makoma ga kasar ta tsakiyar Afrika.

Zaben, wanda a baya ya fuskanci matsaloli na yawan sauye sauyen ranakun gudanar da zaben, ana fata zaben na Kongo zai samar da mutumin da zai gaji shugaban kasar mai ci Joseph Kabila, kana ana sa ran zaben zai tabbatar da sauya shugabancin kasar cikin lumana.

Sai dai kuma, ana fargabar yiwuwar rashin ingancin zaben sakamakon wasu matsaloli dake shafar wasu hukumomin kasar da kuma matakin da gwamnatin kasar ta dauka na hana masu kada kuri'a kimanin miliyan 1 samun damar zaben saboda barazanar da ake da ita ta barkewar cutar Ebola mai saurin kisa a yankin gabashin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China