in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tauraron dan adam na Chang'e-4 na Sin zai isa duniyar wata
2018-12-30 15:52:45 cri

Tauraron dan adam samfurin Chang'e-4 wanda kasar Sin ta harba sararin samaniya yana shirin sauka a duniyar wata da sanyin safiyar yau Lahadi a karon farko da tauraron din zai isa bangaren duniyar watan, hukumar kula da sararin samaniyar kasar (CNSA) ne ta sanar da hakan.

An tabbatar da cewa, tauraron dan adama mai binciken duniyar watan ya riga ya shiga wani yanki na duniyar watan da nisan kilomita 15 da kuma wani bangare na duniyar watan da nisan kilomita 100 da misalin karfe 8:55 na safe agogon birnin Beijing, in ji hukumar ta CNSA.

Tun lokacin da tauraron na Chang'e-4 ya shiga sararin samaniya a ranar 12 ga watan Disamba, cibiyar dake lura da tafiyar tauraron dan adam din dake Beijing ta tabbatar da tafiyar tauraron dan adam din har sau biyu, kana ta gwada yadda ake samun musayar bayanai tsakanin cibiyar da na'urorin isar da sakonni dake jikin tauraron dan adam na Queqiao, ko kuma Magpie Bridge, wanda ake tafiyar da ita a sararin samaniyar halo orbit a kusa da wani yanki na biyu na Lagrangian (L2) na tsarin duniyar wata.

A cewar hukumar ta CNSA, cibiyar tana da ikon zabar lokacin da ya fi dacewa tauraron dan adam din ya sauka a duniyar watan.

An harba tauraron dan adam din samfurin Chang'e-4, ta hanyar amfani da na'urar harba tauraron dan adam ta Long March-3B a ranar 8 ga watan Disamba, daga cibiyar harba tauraron dan adam dake Xichang a kudu maso yammacin lardin Sichuan na kasar Sin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China