in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya bukaci a samar da yanayi mai cike da kwanciyar hankali domin zaben DRC
2018-12-29 17:15:17 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira ga dukkan bangarorin jamhuriyar demokradiyyar Kongo (DRC) da su tabbatar da samar da yanayi mai cike da kwanciyar hankali domin samun nasarar babban zaben kasar dake tafe a ranar Lahadi, kakakin MDDr ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

A yayin da ake shirye shiryen gudanar da zaben shugaban kasar ta DRC, da na majalisar dokokin kasar da kuma na wakilan yankunan kasar, "babban sakataren ya bukaci hukumomin kasar ta DRC, da shugabannin dukkan bangarorin jam'iyyun siyasar kasar, da jami'an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar da kuma kungiyoyin fararen hula dasu cigaba da yin aiki tare domin tabbatar da ganin an samu kyakkyawan yanayin zaman lafiya don baiwa dukkannin masu zabe damar kada kuri'unsu cikin kwanciyar hankali a ranar zaben,"inji sanarwar.

An jima ana sauya ranar gudanar da zaben na DRC. A ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2016 aka cimma matsaya da shugaban kasar mai ci Joseph Kabila, wanda yake kan karagar mulkin kasar tun a shekarar 2001, inda aka cimma matsaya za'a gudanar da zaben kasar a shekarar 2017.

Sai dai an jinkirta zaben bisa dalilai na rashin kayayyakin gudanar da aikin zaben, gami da yawan tashe tashen hankula da suka addabi sassan kasar. A watan Nuwambar 2017, hukumar zaben kasar ta tsara jadawalin gudanar da zaben wanda ya kunshi zaben shugaban kasa, majalisun dokoki da kuma shugabannin lardunan kasar a ranar 23, ga watan Disambar shakarar 2018.

To sai dai kuma, a sakamakon tashin gobara wacce ta yi sanadiyyar kone dubban na'urorin gudanar da aikin zaben wanda aka kaisu Kinshasa, babban birnin kasar, hukumar zaben kasar ta ayyana ranar 30 ga watan nan na Disamba a matsayin ranar zaben don ta samu karin lokacin shirya zaben.

A ranar Laraba kuma, hukumar zaben ta sanar da cewa, an dage zaben a wasu yankunan kasar dake fama da tashe tashen hankulla.

Sai dai duk da hakan, za'a gudanar da zaben a sauran wurare, kana za'a rantsar da sabon shugaban kasar da aka zaba a ranar 18 ga watan Janairun shekara mai zuwa kamar yadda aka tsara, in ji hukumar zaben kasar ta Kongo.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China