Kamfanin dillancin labaran Najeriya wato NAN ya ce, marigayi Alhaji Shehu Shagarin ya zama shugaban Najeriya a Jamhuriyar ta biyu daga shekara ta 1979 zuwa ta 1983, ya rasu bayan ya sha fama da wata cuta wadda ba'a bayyanata ba a babban asibitin kasa dake Abuja.
Iyalan marigayin sun sanar da cewa za'a yi jana'izarsa a yau Asabar a mahaifarsa dake jihar Sokoto a arewacin Najeriya.
An haifi marigayin Aliyu Usman Shehu Shagari a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 1925 a kauyen Shagari cikin jahar Sokoto, wanda ya taba aiki a matsayin malamin makaranta na wani gajeren lokaci kafin daga bisani ya tsunduma fagen siyasar Najeriya a shekara ta 1951.
Sa'annan a shekara ta 1954, an taba zabarsa a matsayin dan majalisar wakilai ta tarayya. Ya taba aiki a matsayin minista da kwamishinan tarayya na tsawon shekaru bakwai daga shekara ta 1958 zuwa ta 1975, kafin daga bisani aka zabe shi shugaban kasa a shekarar 1979.
An hambarar da gwamnatin Shagari a wani juyin mulkin soji, inda Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasar na mulkin soji.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar tsohon shugaban kasar a matsayin babban rashin mutum mai kishin kasa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yiwa al'umma hidima wanda ba za'a taba mantawa da irin gudunmowar da ya baiwa kasar ba.(Murtala Zhang)