Habasha ta kwashe 'yan kasarta ne daga kasashen Tanzania, Libya da kuma hadaddiyar daular larabawa (UAE).
Da yake jawabi ga 'yan jaridu na ciki da wajen kasar, Meles Alem, kakakin ma'aikatar ta MoFA, yace gwamnatin ta samu nasarar kwashe 'yan kasar ne bisa hadin gwiwa da hukumomin kasashen Tanzanian, Libyan da UAE.
Rahotanni sun ce dubban 'yan kasar Habasha ne ake yin safararsu zuwa kasashen waje a duk shekara.
Masu yin safarar bil adama suna bi ne ta wasu hanyoyi 3, da suka hada da shiyyar arewacin kasar zuwa Sudan, Libya da bahar Rum inda suke tsallakawa Turai.
Hanya ta biyu itace ta gabashin kasar ta hanyar Somalia, Djibouti da tekun Red Sea inda suke tsallakwa zuwa kasar Saudi Arabia.
Hanya ta uku itace ta kudancin kasar ta Kenya, Tanzania da Mozambique inda suke bullewa zuwa kasar Afrika ta kudu.