Tun lokacin da kasar Sin ta harba tauraron dan Adam na BeiDou na gwaji na farko a shekara ta 2000, kawo yanzu, kasar Sin ta harba taurarin dan Adam da yawansu ya kai 43 zuwa sararin samaniya, al'amarin da ya sa ta kammala aikin samar da hidimar taswira na tauraron dan Adam ga kasar Sin, da yankin Asiya da na Pasifik, da yankunan dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya har ma ga duniya baki daya.(Murtala Zhang)