in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kara fitar da sana'ar ba da hidima zuwa kasashen waje
2018-12-28 10:58:05 cri
Alkaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar a jiya Alhamis, sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Nuwamban bana, jimillar kudin shigi da ficen sana'ar bada hidima ta kasar ta wuce kudin Sin Yuan triliyan 4.7, wadda ta karu da kashi 11.5 bisa dari idan aka kwatanta da ta makamancin lokacin bara. Kana, yawan kudin sana'ar ba da hidima ya kai sama da kashi 30 bisa dari, wanda ya kai matsayin koli a tarihi.

Mai magana da yawun ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, bunkasuwar ayyukan shige da ficen sana'ar ba da hidima na shaida cewa, tattalin arziki irin na sana'ar ba da hidima na bunkasa yadda ya kamata, kuma tasirin kasar Sin a duk fadin duniya a wannan fanni ya taimaka sosai ga bunkasuwar ayyukan fitar da sana'ar ba da hidima ta kasar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China