in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin za ta taimaka wajen aiwatar da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa
2018-12-28 10:52:43 cri
A halin yanzu kasar Sin na nan na kokarin amincewa da dokar zuba jari kan baki 'yan kasuwa. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, Gao Feng ya bayyana cewa, dokar za ta kara samar da cikakken tabbaci ga baki masu zuba jari da kamfanonin kasashen waje wajen kare hakkokinsu, da kyautata yanayin zuba jari na kasar Sin, da kuma saukakawa baki 'yan kasuwa yadda za su zuba jari bisa doka a kasar ta Sin.

Gao Feng ya ce, gwamnatin kasar Sin ta dade tana mai da hankali kan kare hakkokin masu zuba jari gami da kamfanoni na kasashen waje, da kara kokarin kare hanyar tsarawa gami da kyautata wasu dokoki da ka'idoji.

Gao ya ce, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin za ta taimakawa majalisar wakilan jama'ar kasar wajen gudanar da aikin nazartar dokar, da gaggauta zartas da ita, ta yadda za'a samar da yanayin zuba jari mai inganci da adalci kuma ba tare da rufa-rufa ba ga baki masu sha'awar zuba jari a kasar Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China