in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sana'ar sadarwar zamanin kasar Sin za ta karu da kashi 140 bisa dari a bana
2018-12-28 10:51:29 cri
Rahoton jaridar People's Daily ta kasar Sin ta ruwaito, ministan kula da masana'antu da harkokin sadarwa na kasar Sin Miao Wei yana bayyanawa a wajen taron bitar ayyukan masana'antu da sadarwa na kasar da aka yi kwanakin baya cewa, bisa hasashen da aka yi, a shekarar da muke ciki, sana'ar sadarwar zamani za ta karu da kashi 140 bisa dari, kana, yawan kudin shigar da za a samu daga ayyukan Intanet zai karu da kashi 18 bisa dari, a kasar ta Sin.

Miao ya ce, a bana, an riga an cimma burin kara saurin amfani da Intanet tare kuma da rage yawan kudin da ake kashewa wajen amfani da Intanet, wanda aka tsara shi a cikin rahoton aikin gwamnati. Har wa yau, an bayar da kyakkyawar hidima ta fuskar sadarwar zamani a kasar, inda adadin yawan kauyukan da aka saka musu layukan Intanet ya karu zuwa kashi 98 bisa dari, kuma adadin yawan kauyuka masu fama da talauci da aka shimfida musu layukan Intanet na zamani ya kai kashi 95 bisa dari.

Miao ya kara da cewa, a shekara mai kamawa wato 2019, gwamnati za ta ci gaba da kyautata ayyukan samar da hidimomin sadarwar zamani, don kokarin cimma burin saka layukan Intanet masu sauri na zamani a kashi 98 bisa dari na kauyuka masu fama da talauci a fadin kasar Sin. Kana, za'a gaggauta amfani da fasahar sadarwar 5G, da gudanar da sauran wasu ayyukan da abun ya shafa yadda ya kamata, tare kuma da yin kirkire-kirkire a fannin harkokin sadarwa.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China