in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Congo-Kinshasa ta kori jakadan EU daga kasar
2018-12-28 10:20:59 cri
Mataimakin firaministan kasar Congo-Kinshasa, kana ministan harkokin waje da dunkulewar yankin da kasar ke ciki, Leonard Okitundu ya sanar a jiya Alhamis cewa, gwamnatin kasar ta bukaci jakadan kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU dake Congo-Kinshasa da ya tafe daga kasar, domin mai da martani ga kungiyar EU bisa matakin kungiyar na tsawaita takunkumin da ta kakabawa wasu 'yan kasar 14.

Kwanan baya ne, majalisar zartaswar kungiyar EU ta sanar da cewa, za ta tsawaita takunkumin da ta sanyawa 'yan kasar Congo-Kinshasa guda 14 zuwa ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2019, ciki har da matakan rike kudade da kadarorinsu da kuma hana su shiga cikin kasashen kungiyar EU. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China