in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majinyata 24 Sun Tsere Daga Cibiyar Masu Cutar Ebola Ta Kasar Kongo
2018-12-28 09:44:56 cri
Jami'an lafiya karkashin ma'aikatar lafiya ta kasar Kongo, sun ce a kalla mijinyata mutum 24 ne suka tsere daga sansanin da aka tanada don kula da masu fama da cutar Ebola, shi wannan sansanin yana karkashin kulawar cibiyar kula da cutar Ebola ne dake garin Beni.

Amma jami'an lafiyar sun ce majinyatan sun tsere ne daga sansanin sakamakon garin da masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da soke zaben shugaban kasa da aka yi ranar Lahadin da ta gabata a garin dake gabashin kasar ta Kongo.

Wasu daga cikin mutanen gwajin da aka musu ya tabbatar ba sa dauke da cutar ta Ebola, inda wasu daga cikinsu ba a kai ga gwada su ba, uku daga cikin majinyatan sun dawo cibiyar, inda ma'aikatan lafiya suke ta kokarin hada kan sauran majinyatan don dawo da su sansanin.

Ma'aikatan lafiyar sun ce suna da bayanan majinyatan da lambobin wayarsu gaba daya, don haka za su yi kokarin ganin sun nemo su don dawowa da su sansanin don ci gaba da karbar magani da kuma gwajin cutar ta Ebola.(Labarin da aka samu daga jaridar Leadership)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China