in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasuwar motoci masu amfani da sabbin makamashi ta kasar Sin za ta ci gaba da bunkasa cikin sauri a badi
2018-12-27 20:09:25 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, Gao Feng ya bayyana a yau Alhamis cewa, daga watan Janairu zuwa Nuwambar bana, adadin yawan motoci masu amfani da sabbin makamashi da aka sayar ya wuce miliyan daya a kasar Sin, wanda hakan ke nuna adadin ya karu da kashi 68 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.

Sakamakon ci gaban fasahohi, da amincewar masu sayayya, gami da kyautatuwar muhimman ababen more rayuwar jama'a, an yi hasashen cewa, a shekara mai kamawa wato 2019, kasuwar cinikin motoci masu amfani da sabbin makamashi a kasar Sin za ta kara habaka da bunkasa cikin saurin gaske.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China