in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Kasar Sin za ta yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka keta hakkin mallakar kira
2018-12-27 17:16:46 cri


Hukumar tsara dokoki ta kasar Sin suna tantance wani daftarin dokar da ya shafi yadda za a kare hakkin mallakar kira, sa'an nan wanda ya keta hakkin dokar zai fuskanci hukunci na biyan tara. Wata daya kafin lamarin, an yanke hukunci kan wata karar da aka yi mai alaka da batun keta hakkin mallakar kira a fannin wata fasahar samar da na'urori masu dauke yiwa baturin wayar salula caji, inda aka dakatar da aikin wani kamfanin da ya aikata laifin satar fasahohi na sauran, da biya kudin da ya kai kudin Sin RMB Yuan miliyan 2 ga kamfanin da ya samu hasara sakamakon keta hakkinsa da aka yi masa.

Yadda kasar Sin take neman daidaita dokar mai alaka da kare hakkin mallakar kira, shi ne karo na 4 da kasar ta yi garambawul kan dokar, wanda aka gabatar da ita a shekarar 1985. Sabon daftarin dokar ya kunshi fannoni 6 masu muhimmanci, cikinsu har da kara biyan kudi, wanda za a iya ninka hasarar da aka samu sau 5, wanda ya kai Yuan miliyan 5, da kuma kyautata dabarar da ake dauka wajen aiwatar da dokar kare hakkin mallakar kira.

An tabbatar da cewa, dole mai take hakkin mallakar fasaha ya gabatar da takardun shaidar da abin ya shafa, kana idan an take hakkin mallakar fasaha kan yanar gizo, dole mai samar da hidima kan yanar gizo ya hana aikata laifin cikin lokaci, in ba haka ba, za a yi masa hukunta tare da mai take hakkin mallakar fasahar, ban da haka kuma, za a samar da kudin yabo ga wadanda suka kira sabbin kayayyaki, har za a tsawaita lokacin mallakar fasahar zanen siffar kayan daga shekaru goma zuwa sha biyar.

Daga wadannan abubuwan da aka gyara a cikin dokar, an lura cewa, makasudin gyaran dokar a kasar Sin shi ne domin biyan sabbin bukatunta a halin yanzu tare kuma da warware matsalolin da take fuskanta a fannin kiyaye ikon mallakar fasaha, haka kuma za a kiyaye hakkin halal na masu kera sabbin kayayyaki da kyautata tsarin sa kaimi kan aikin kira, ta yadda za a cimma burin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci a kasar Sin.

An kuma kafa dokar "diyyar horo", domin kare 'yancin mallakar lambar kira. A halin yanzu, ban da dokar kiyaye ikon masu sayayya, a mafi yawan lokaci, ana neman diyya bisa ka'idar biyan diyya bisa asarar da aka yi. Amma a fannin dokar kare ikon mallakar ilmi kuma, iri wannan ka'ida ba za ta iya biyan bukatun masu neman biyan diyya ba, saboda wasu sabbin matsalolin da aka gamu da su da kuma wasu miyagun laifukan da aka aikata a wannan fanni.

Tun a shekarar bana, sau da dama, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin za ta kyautata ayyukanta wajen gudanar da bincike kan ikon mallakar ilmi, yayin da kafa dokar "diyyar horo" a kasa, domin kara diyyar da masu aikata laifuffuka za su biya.

Gyararren shirin doka kan hakkin mallakar kira ya tanadi cewa, game da mutanen da suka ketawa sauran mutane hakkinsu na ikon mallakar kira, za su biya kudin diyyar da yawansu zai iya ninkawa sau daya zuwa sau biyar na yawan hasarar kudin da za'a samu. Idan ba'a iya kirga kudin diyyar da sauki ba, kotu zata yanke hukunci, kuma yawan kudin diyyar da za'a biya zai karu daga Yuan dubu goma zuwa Yuan miliyan daya, har zuwa Yuan dubu dari zuwa Yuan miliyan biyar. Irin wannan kudin diyyar mai tsanani da za'a biya, zai sa masu keta hakkin mallakar kira za su dandano kudarsu sakamakon laifin da suka aikata, ta yadda ba za su sake aikata laifin ba, da kuma tabbatar da bin doka da oda da adalci tsakanin zamantakewar al'umma, saboda a cewar malam Bahaushe, rigakafi ya fi magani.

Har wa yau, sake gyaran dokar kare hakkin mallakar kira da kasar Sin ta yi a wannan karo, zai yi babban tasiri ga kara ingancin neman hakkin mallakar kira.

Rahoton da hukumar kula da hakkin mallakar ilmi ta duniya ta bayar, an ce, a shekarar 2017, yawan lambobin kira da ake neman hakkin mallakarsu a wurin hukumar kula da hakkin mallakar ilmi ta kasar Sin ya karya matsayin bajinta, wanda har ya kai miliyan daya da dubu 380, kuma kasar Sin ta zama ta farko a duniya ta fannonin yawan lambobin kira da tambura da zanen fasalin kayayyakin masana'antu da ake neman hakkin mallakarsu. Sai dai a sa'i daya, akwai matsalar rashin inganci da ake fuskanta ta fannin fasahohin da ake neman hakkin mallakarsu, abin da ke bukatar a yi ta inganta dokokin da abin ya shafa.

A halin da ake ciki yanzu, dan Adam na cikin wani juyin juya hali na kirkire-kirkiren fasahohi da gyare-gyaren masana'antu, abin da ya kara yaukaka dangantakar dake tsakanin aikin kare hakkin mallakar ilmi da kuma aikin kirkire-kirkiren fasahohi.

A matsayinta na daya daga cikin jerin kasashen dake sahun gaba a duniya wajen yin kirkire-kirkire, kasar Sin ta kara kiyaye ikon mallakar fasaha ba domin biyan bukatun cikin gida wajen gaggauta canja hanyar ci gaban tattalin arziki, da gudanar da tsare-tsaren samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire kawai ba, har ma domin biyan bukatun dake wajaba na kara bude kofa ga kasashen ketare.

Kiyaye ikon mallakar fasaha wato kiyaye ayyukan yin kirkire-kirkire. A matsayin wata muhimmiyar doka ta inganta yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, an kara gyara dokar lambar kira har sau hudu, wannan ya nuna aniyar kasar Sin na inganta kiyaye ikon mallakar fasaha shekaru 40 tun bayan soma yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, yana dacewa da bukatun dake akwai wajen yin kwaskwarima na sabon zagaye kan kimiyya da fasaha da kuma masana'antu, tare kuma da dacewar bukatun kasar na neman ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire. Yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka keta hakkin mallakar kira da kasar Sin za ta yi zai kara inganta Sinawa wajen yin kirkire-kirkire, da kuma bada kariya ga kasar wajen samun ci gaba mai inganci. (Jamila Zhou, Maryam Yang, Murtala Zhang, Bilkisu Xin, Lubabatu Lei, Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China