A ranar 30 ga watan nan da muke ciki, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar dokokin kasar da kuma zaben mambobin majalisun dokokin jihohi a kasar ta Congo-Kinshasa.
Kwamitin kula da harkokin zabe mai zaman kansa na kasar ya fidda sanarwa a ranar 26 ga wata cewa, za a jinkirta ayyukan jefa kuri'u a wasu wuraren dake arewa masu gabashi da kuma yammacin kasar zuwa watan Maris na shekara mai zuwa. A sa'i daya kuma, ya ce, za a gabatar da sakamakon babban zaben shugaban kasa a ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 2019, sa'an nan, za a rantsar da sabon shugaban kasa a ranar 18 ga watan Janairu na shekarar 2019. (Maryam)