in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar siyasar kwamitin tsakiya na JKS ta kira taron demokuradiyyya
2018-12-27 10:54:20 cri

Hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta shirya taron zaman rayuwar demokuradiyya a tsakanin 25 zuwa 26 ga wata, shugaban kasar Xi Jinping ya shugabanci taron tare kuma da ba da muhimmin jawabi.

A yayin taron, an nuna cewa, tabbatar da muradun da aka tsara a babban taron wakilai karo na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da tabbatar da zaman al'umma mai matsakaicin karfi a dukkan fannoni, da kafa wata kasar Sin mai karfi na zamani irin na gurguzu, da kuma tabbatar da burin jama'ar kasar na samun kyautattuwar zaman rayuwa, sun kasance buri ne na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a sabon zamani.

Baya ga haka, an jadadda cewa, ko da yaushe ana mai da hankali kan halin jam'iyyar, dole ne a kiyaye hali mai kyau na jam'iyyar da na siyasa, dole jami'an hukumar siyasar kwamitin tsakiya sun nuna da'a da mutunta kai, don ba da jagoranci a fannin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China