Wannan sabon shirin ya kunshi wasu ayyuka fiye da 80, wadanda suka shafi hukumomin kasar guda 10.
Yayin sanar da wannan shirin, ofishin firaministan kasar Abiy Ahmed ya bayyana cewa, shirin zai zama karkashin sa idon sashi mai kula da tsara manufofi da gudanar da su na ofishin firaministan kasar, tare da hadin gwiwar hukumar zuba jari ta kasar EIC.
A cewar firaministan, sabon shirin shi ne wani bangare na babban shirin kasar na samar da karin guraben aikin yi. (Bello Wang)