in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Janyewar sojojin Amurka daga Syria zai sassauta yanayin yankin, in ji Rasha
2018-12-27 10:41:47 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana a jiya Laraba cewa, janyewar sojojin Amurka daga kasar Syria zai ba da taimako wajen sassauta yanayin yankin bisa dukkan fannoni.

Ta bayyana haka ne yayin taron manema labaran da aka saba yi, ta kuma kara da cewa, kwanan baya, kasar Amurka ta tsaida kudurin janye sojojinta daga kasar Syria. A halin yanzu, kasar Rasha tana mai da hankali matuka kan yadda kasar Amurka take aiwatar da wannan aiki, sabo da ta san muhimmiyar ma'anar wannan al'amari. A daya bangaren kuma, kasar Rasha ba ta san jadawalin kasar Amurka na janye sojojinta daga kasar Syria ba. Bugu da kari, ta ce, ya kamata kasar Amurka ta mika yankin da sojojinta suka mamaye ga gwamnatin kasar Syria, bayan janyewar sojojinta daga kasar, amma ya zuwa yanzu, Amurka da Syria ba su yi shawarwari kan wannan batu ba.

A ranar 19 ga wata, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da cewa, Amurka ta fara janye sojojinta daga kasar Syria bisa kyakkyawan sakamakon da ta cimma wajen yaki da kungiyar IS a kasar Syria. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China