in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya yi rangadi a sansanonin sojojin kasarsa dake Iraki
2018-12-27 10:28:42 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi rangadi a sansanonin sojojin kasarsa dake kasar Iraki, inda ya taya sojojin murnar bikin Krismati, kamar yadda gidan telabijin din kasar Irakin ya sanar a jiya Laraba.

Cikin labarin da gidan telabijin din ya bayar, an ce shugaba Trump ya ce ba shi da shirin janye sojojin kasar Amurka daga kasar ta Iraki.

A nata bangaren, sakatariya mai kula da aikin watsa labarai a fadar shugaban kasar Amurkan ta White House, Sarah Sanders, ta bayyana ta kafar sada zumunta ta Twitter cewa, "Trump da uwargidansa sun kai ziyara a Iraki a daren da ake bikin Krismati, inda ya gana da sojojin kasar, gami da manyan hafsoshi, don jinjina musu kan gudunmowar da suka bayar, da nasarorin da suka samu, gami da taya su murnar bikin Krismati."

Hakan ya kasance karon farko da shugaba Trump ya ziyarci kasar Iraki tun bayan da ya hau karagar mulki kusan shekaru 2 da suka wuce. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China